Wata mata mai shekara 40 a ƙauyen Garin Mallam, ƙaramar hukumar Guri ta jihar Jigawa, ta cinna wa kanta wuta bayan mijinta ya sake ta. DSP Lawan Shiisu, jami’in hulɗa da jama’a na Ƴansandan jihar, ya tabbatar da faruwar lamarin a wata sanarwa da ya fitar a yau Juma’a a Dutse.
Shiisu ya bayyana cewa matar ta zuba fetur a jikinta kuma ta cinna wa kanta wuta a bayan gari. ‘Yansanda sun samu rahoto da misalin karfe 7:40 na safiyar Alhamis, inda suka isa wurin suka tarar da gawar matar ta kone kurmus. Binciken farko ya nuna cewa mamaciyar ta daɗe tana fama da damuwa tun bayan da mijinta ya sake ta. ‘Yansanda sun kwashe ƙonanniyar gawar sannan suka miƙa wa iyalanta don yin jana’iza.
- Ambaliyar Ruwa: Mutane 16 Sun Rasu, 3,936 Sun Rasa Matsugunansu A Jigawa – SEMA
- Ambaliyar Ruwa Ta Yi Ajalin Mutane 30, Ta Raba Dubbai Da Gidajensu A Jigawa
Da yake mayar da martani kan wannan abin tausayi, kwamishinan Ƴansandan jihar Jigawa, Ahmadu Abdullahi, ya yi kira ga jama’a su nemi shawara da taimako a lokutan da suke cikin damuwa ko wata wahala, tare da jaddada muhimmancin dogaro da Allah wajen warware matsalolinsu.