A cikin zango na uku na shekarar 2023 a karkashin gwamantin Shugaban kasa Bola Tinubu, ma’aikatar tsaro ta karbi naira biliyan 412, ma’aikatar kula da harkokin ‘yansanda ta karbi naira biliyan 150, ofishin mai bai wa shugaban kasa shawara a fannin tsaro, ya karbi naira biliyan 31, inda ma’aikatar kula da harkokin cikin gida ta samu naira biliyan 64, jimlar naira tiriliyan 3.2 aka zuba a fannin tsaron kasar a cikin shekara daya.
A bisa wani bincike da kafar Sahara Reporters ta yi wanda Punch ta wallafa, a 2023, jimlar naira biliyan 657, aka bai wa sashen tsaro a zango na uku.
- Huawei Ya Kaddamar Da Horo Game Da Tsaron Yanar Gizo Ga Jami’an Zimbabwe
- Kaico: Wata Mata Ta Bankawa Kanta Wuta A Jigawa
Kazalika, a zango na hudu ma’aikatar tsaro ta karbi naira biliyan 487, ma’aiktar kula da harkokin ‘yansanda ta karbi naira biliyan 282, ma’aikatar kula da harkokin cikin gida ta karbi naira biliyan 119, inda ofishin ma’aikatar tsaro ta karbi naira biliyan 113.
Jimilar naira tiriliyan daya aka bai wa hukumomin tsaro da kuma ma’aikatun tsaro a zango na hudu na 2023.
Hakan ya nuna cewa daga zango na uku zuwa na hudu na 2023, jimlar naira tiriliyan 1.657 aka bai wa hukumomin tsaro da ma’aikatu.
A bisa nazarin da aka yi na biyan kudaden da gwamnatin tarayya ta yi, ya nuna cewa daga watan Janairu zuwa Yuni na tsakiyar shekarar 2024, jimilar naira 1.032 tiriliyan aka bai wa ma’aiktar tsaro.
Akwai kuma karin wasu naira biliyan 424 da gwamnatin ta bai wa ma’aikatar kula da harkokin ‘yansanda, inda kuma aka bai wa ofishin mai bai wa shugaban kasa shawara naira biliyan 223. Wannan ya kai jimlar naira triliyan 1.6, da aka bayar a cikin watannin shida.
Gaba dayan wadannan kudaden da gwamnatin ta bayar a cikin watannin shida, rundunar soji kasa ta samu naira biliyan 426, inda rundunar sojin ruwa aka ba ta naira biliyan 140, sai kuma rundunar sojin sama an ba ta naira biliyan 121. Sannan hukumar leken asiri an ba ta naira biliyan 13.7.
A zango na uku 2023 da kuma a zango na biyu na 2024, gwamnatin ta bai wa ma’aikataun tsaro da hukumomin tsaro naira tiriliyan 3.2.
Baya ga gwamnatin tarayya da take bayar da kudade, haka suma gwamnatocin jihohi na bayar da kudade don a magance kalubalen na rashin tsaro a jihohinsu.
Duba da ci gaba da samun karuwar kalubalen rashin tsaron a kasar nan ne ya sanya jihohin da ke a kudu maso yammacin kasar nan, suka fara kirkiro da nasu jami’an tsaron na sa-kai da suka yi wa lakabi da “Amotekun”.
A cikin kasar nan, fannin tsaro na daga cikin jeren ayyukan da gwamnatin tarayya ke kula da shi.
Wasu na cewa, kwalliya na biyan kudin sabulu biyo bayan kirkiro da jami’an tsaron na sa-kai, sai dai, duk da haka akwai sauran rina a kaba na kalubalen rashin tsaron a yankin na kudu maso yamma.
Wasu mata a Jihar Ondo, sun gudanar da zanga-zangar lumana a tsirara, saboda satar manoma da ake yi a gonakansu.
Gwamnatin Ondo ta kashe naira biliyan 3.6 a kan jami’an tsaron sa-kai na Amotekun a cikin watanni 27, amma duk da haka, al’ummomin yankin na ci gaba da zama a cikin fargaba.
Gwamnatin Jihar Osun ta yi kasafin naira miliyan 100 a kan jami’an tsaron sa-kai na Amotekun a 2024, inda ya zuwa yanzu gwamnatin ta kashe naira miliyan 39 a cikin wata shida a 2024.
Jihohi da dama sun zuba makudan kudade a kan jami’an tsaro na sintiri da suka kirkiro da su, inda har wasun su suka kakkafa ma’aikatar tsaro na cikin gida suka kuma jibga dimbin kudade, amma har yanzu lamarin kamar jiya iyau.
Misalil, a Jihar Katsina da ke a arewa maso yamma, gwamnatin jihar ta yi kasafin kudi na naira biliyan 3.4 a cikin harkokin tsaro na cikin gidanta a 2024, inda ya zuwa yanzu, ta kashe naira miliyan 514 a cikin watanni shida.
Haka takwararta ta Jihar Kaduna da ke a yankin na arewa maso yamma, ta zuba naira biliyan 15.4 ga ma’aikatar kula da harkokin tsaronta na cikin gida a 2024.