Gwamnatin tarayya ta amnince da a mika Naira Biliyan 2.5 daga Bankin Masana’antu zuwa Gidauniyar Bunkasa Ma’adanai, domin tabbatar da ci gaban sashin.
Ana sa ran kudin ya taimaka wajen tallafa wa masu hakar ma’adanai na cikin gida shiga domin a dama dasu yadda ya kamata.
- Zaben Shugabanni: Sabon Rikici Ya Kunno Kai A PDP
- Durkushewar Kamfanoni Ta Kara Rashin Aikin Yi Tsakanin Matasa
Ministan Ma’adanai, Dr Dele Alake, ya bayyana haka yayin wani tarona awa 3 da ya yi da masu ruwa da tsaki a bangaren ma’adanai.
Sanarwar haka ya fito ne daga mai ba Ministan shawara a kan watsa labarai, Segun Tomori, ya kuma kara da cewa, a ranar Juma’a aka yi taron inda aka tattauna abubuwan da suka faru a sashin a ‘yan kwanakin nan wanda suka hada da karin kudin lasisi da sakamakon da hakan ya haifar.
Sanarwa ta kuma ci gaba da bayyana cewa, “A wani muhimmin mataki kuma, gwamnati ta amince da cire naira Biliyan 2.5 daga Bankin Masana’antu zuwa gidauniyar ma’adanai, ana sa ran wannan kudaden za su taimaka wa masu hakar ma’adanai na cikin gida gudanar da harkokinmsu yadda ya kamata musamman ganin yadda ‘yan kasashen waje ke babakere a sashin.”
Sanarwar ta kuma kara da cewa, gwamnati ta amince da sake rage kudin lasisin da aka kara kwanakin baya domin kowa ya san ana yi da shi.”
Tun da farko shugaban kungiyar masu hakar ma’adanai ta kasa, Chief Dele Ayanleke, ya gabatar da bukatunsu wadanda suka hada da yadda gwamnonin jihohi ke musu katsalanda ta hanyar kafa dokoki da yadda ayyukan Dogaran Kula da hakar ma’adanai ‘Mining marshals, ke kawo musu cikas da kuma yadda aka yi watsi da masu ruwa da tsaki wajen yi wa dokokin hakar ma’adanai kwaskwarima.
Taron ya samu halartar masu ruwa da tsaki a bangaren hakar ma’adanai daga sassan kasar nan.