Allah ya yi wa mai martaba Sarkin Ningi, Alhaji (Dr.) Yunusa Muhammad Danyaya OON, rasuwa ya na da shekaru 88 a duniya.
Sarkin Mai daraja ta 1 ya shafe fiye da shekaru 40 a ƙaragar mulki, ya rasu da safiyar ranar Lahadi.
- Mashawarcin Shugaban Amurka Kan Harkokin Tsaro Jake Sullivan Zai Ziyarci Kasar Sin
- Wace Wainar Ake Toyawa A Jihar Kaduna?
Rasuwar, babbar giɓi ce da ya bar wa al’ummar masarautar Ningi ta jihar Bauchi da ma ƙasa baki ɗaya, domin kuwa ya kasance sarki mai kima da mutunci a idon ɓangarorin al’umma daban-daban.
An shirya cewa, za a yi wa Marigayin sallar jana’iza da ƙarfe 4 na yammaci yau Lahadi a masarautar Ningi kamar yadda addinin Musulunci ya tanadar.
A saƙon ta’aziyya da ya fitar cikin gaggawa, gwamnan jihar, Bauchi Bala Muhammad, ya koka da rashin tare da misalta Sarkin a matsayin jigon son zaman lafiya, adali wanda ya himmatu wajen kyautata jin daɗi da walwalar al’ummarsa.
Ya ce, a tsawon shekarun da ya shafe a mulki, ya kasance mai gudanar da mulki abun koyi, inganta haɗin kai, cigaba, zaman lafiya da kuma bunƙasar masarautar Ningi.
A cewar Gwamnan, tsarin mulkin marigayi ya taimaka sosai wajen kiyaye darajar sarauta, al’adu har ma da mutunta addinin musulunci, kuma hakan zai zama abun cigaba da koyi ga hakan ga ‘yan baya masu zuwa.
A kan wannan, ta cikin sanarwar da kakakinsa, Mukhtar Gidado ya fitar, gwamnan ya miƙa ta’aziyyarsa ga masarautar Ningi, iyalan mamacin da ma ɗaukacin al’ummar jihar Bauchi bisa wannan babban rashin da aka yi.
Ya nuna cewa za su cigaba da tuna Sarkin a matsayinsa na uba, jigo a rayuwarsu wanda ya taka muhimmiyar rawa wajen cigaban jihar Bauchi da ma Nijeriya.
Ya yi addu’ar Allah ya jiƙan marigayi Sarki ya sanya shi cikin Aljanna maɗaukakiya.