Asusun ba da lamuni na ilimi na Nijeriya (NELFUND) ya bayyana cewa, Hon. Lanre Laoshe, wanda tsohon wanda ya ci gajiyar shirin bayar da lamuni na dalibai na Gwamnatin Tarayya ne, ya biya bashin Naira 1,200 da ya karba a tsakanin 1976 zuwa 1979, da kudi Naira miliyan 3,189,217.
A cewar sanarwar da NELFUND ta fitar, Hon. Laoshe, wanda fitaccen tsohon dan majalisar wakilai ne kuma tsohon mataimakin mai tsawatarwa a majalisar, wanda ya ci gajiyar shirin bayar da lamuni na daliban gwamnatin tarayya, ya bayyana matukar jin dadinsa da tallafin kudi da ya samu daga gwamnatin tarayya a lokacin da yake neman ilimi.
- Ambaliyar Ruwa Ta Lalata Gidaje 14,940 A Sokoto
- Sanata Bomai Ya Bada Tallafin Miliyan 20 Da Tufafi Ga Wadanda Ambaliyar Ruwa Ta Shafa A Yobe
Ya bayyana cewa, domin sanin ainihin yadda lissafin naira 1,200 za ta kasance in aka misalta ta a wannan lokacin, Hon. Laoshe ya nemi sanin matsakaicin farashin canji na shekarar 1972 zuwa 1985 daga babban bankin Nijeriya (CBN).
“Lissafin ya nuna cewa, a shekarar 1979, farashin dala akan Naira ya kasance $1.00 daidai take da kusan Kobo 60, ya kama, Naira 1,200.00 ta yi daidai da $2,013.42 a lokacin.
“Amfani da canjin dala a yanzun, $1.00 daidai take da Naira 1,583.98, Hon. Laoshe ya lissafa cewa, kwatankwacin adadin yanzu, zai zama naira miliyan 3,189,217.00.”