Gwamnatin jihar Kaduna ta ce, sojojin da ke sintiri a yankin Kampanin Doka, Birnin Gwari, sun kashe ‘yan bindiga takwas.
Hakan ya fito ne ta bakin kwamishinan sa ido na ma’aikatar tsaro da harkokin cikin gida, Samuel Aruwan a ranar Alhamis.
- Ma’aikaci Ya Mayar Da Dala 10,000 Da Ya Tsinta A Cikin Jirgi A Kano
- ‘Yan Nijeriya Miliyan 31.8 Na Fama Da Matsananciyar Yunwa – Rahoto
Sanarwar ta kara da cewa, a yayin artabun, sojojin sun samu nasarar kwato bindigogin AK-47 guda uku da kuma mujallun AK-47 guda takwas.
Sauran abubuwan da aka kwato a cewar sanarwar sun hada da babura shida, wayoyin hannu guda uku, na’urorin rediyon Baofeng guda biyu, da kuma tufafi guda Uku.
Bugu da kari, sojojin sun kuma sake arangama da wata tawaga a kusa da babban yankin Gayam. Sojojin sun kashe daya, yayin da ake zargin wasu sun tsere da raunukan harbin bindiga.
Gwamnan jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, ya godewa jami’an tsaron, sannan ya yaba wa rundunar a karkashin jagorancin babban kwamandan rundunar sojojin Nijeriya ta daya, Manjo Janar MLD Saraso a bisa samun wannan gagarumar nasara.