An tuhumi wasu mutane 10 da laifin cin amanar kasa da kuma hada baki wajen tunzura sojoji su yi juyin mulki, yayin zanga-zangar matsin rayuwa da ta gudana a fadin Nijeriya.
Wannan na zuwa ne bayan zanga-zangar da aka yi a fadin Nijeriya a watan da ya gabata, inda dubban mutane suka fantsama kan tituna domin nuna adawa da matsalar tsadar rayuwa.
- Ƴan Bindiga Sun Kashe Ɗansanda Da Wani A Sakkwato
- Uwargidan Gwamnan Zamfara Ta Tallafawa Majinyata 1000 Da Abinci Da KuÉ—i
Zanga-zangar ta ci karo da matakin mumunan murkushewa da jami’an tsaro suka dauka kuma kungiyar Amnesty International ta ce akalla mutum 13 sun mutu.
Amma jami’an tsaro sun musanta yin amfani da muggan makamai.
An dai gurfanar da mutanen 10 a gaban babbar kotun tarayya da ke Abuja, inda kuma suka shigar da karar ba su da laifi.
Suna fuskantar hukuncin kisa idan har aka same su da laifi, in ji lauyan kare hakkin dan Adam Inibehe Effiong.
Masu shigar da kara, sun ce a cikin takardun kotun, masu zanga-zangar sun yi nufin kawo cikas ga zaman lafiya a Nijeriya.
“Sun hada baki wajen aikata laifi, da cin amanar kasa”.
Masu gabatar da kara sun kuma gabatar da wasu tuhume-tuhume guda biyar a kan wadanda ake tuhuma a karkashin dokar hukunta manyan laifuka ta kasar, da suka hada da ingiza sojoji su yi juyin mulki.
Sauran tuhume-tuhumen sun hada da kone gine-ginen gwamnati da kuma kawo cikas ga zaman lafiya.
Lauyoyin wadanda ake tuhumar sun nemi a sake su bisa beli, sai dai gwamnatin tarayya ta ki amincewa da hakan.
Kotun, za ta yanke hukunci a ranar 11 ga watan Satumba lokacin da ake sa ran za a fara shari’ar.