Ƙaramin Ministan Tsaro, Dakta Bello Muhammad Matawalle, ya isa jihar Sokoto domin tsaurara matakan tsaro da nufin kawar da ayyukan ‘yan bindiga da suka addabi yankin Arewa maso Yamma.
Matawalle ya samu rakiyar wasu manyan hafsoshin soji da suka hada da babban hafsan tsaron kasa, Janar Christopher Musa, da shugaban hukumar leken asiri ta sojoji, Manjo Janar Emmanuel Undiandeye.
- ‘Yansandan Kano Sun Ceto Wata Budurwa Bayan Shafe Kwanaki 30 A Hannun Masu Garkuwa A Kaduna
- Zanga-zanga: Ana Tuhumar Mutane 10 Da Laifin Cin Amanar Kasa
Bugu da kari, daga cikin ‘yan rakiyar, akwai Birgediya Janar IA Ajose, Babban Hafsan Sojojin (GOC) na Division 8, da sauran manyan jami’an soji.
Ziyarar dai ta yi daidai da umarnin da shugaban kasa ya ba wa hafsoshin tsaro na su koma jihar Sokoto a ci gaba da kokarin inganta tsaro da gudanar da ayyukan soji a yankin.