Sarkin Musulmai, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar, ya ayyana ranar Asabar 30 ga watan Yulin 2022 a matsayin ranar farko ta sabuwar shekarar Musulunci wato 1 ga watan Muharram 1444 AH.
Shugaban kwamitin bayar da shawara ga Majalisar Sarkin Musulmai kan harkokin addinai, Farfesa Sambo Wali Junaidu, shi ne ya shaida hakan ta cikin wata sanarwar da ya fitar a ranar Juma’a.
- Sarkin Musulmi Ya Bukaci Yin Addu’o’i Na Musanman Don Magance Matsalar Tsaro
- Fadar Sarkin Musulmi Ta Ayyana Gobe Alhamis 1 Ga Watan Zul Hajji
Farfesa Sambo, wanda shi ne Wazirin Sokoto, ya kara da cewa, “Kwamitin bayar da shawara kan harkokin addinai na Majalisar Sarkin Musulmai da kwamitin duba wata na kasa ba su samu wani rahoton ganin Jinjirin watan sabuwar shekarar Musulunci na Muharram a sassan kasar nan ba a ranar Alhamis 28 ga watan Yulin 2022, wanda ya zo daidai da 29 ga watan Zulhijja 1443 AH.
“Don haka ranar Juma’a 29th July, 2022 ta kasance ranar 30 ga watan Zulhijja1443AH.”
Sanarwar ta ce ranar Asabar zata kasance ranar farko ta sabuwar shekarar Musulunci.
Kazalika, Sarkin Musulmai ya taya al’umar musulmai murnar shaiga sabuwar shekarar Musulunci tare da nemansu da su kara rokon Allah da ya ci gaba da kawo taimakonsa cikin lamuran kasar nan.
Sultan ya kuma bukaci al’umar musulmai da su ci gaba da yin addu’o’in neman Allah ya kawo karshen matsalolin tsaro da suke addabar Nijeriya tare da fatan shiga sabuwar shekarar Musulunci cikin koshin lafiya.