Bayan samun rahotannin mace-macen mutane a wuraren hakar ma’adanai ba bisa kan ka’ida ba da kuma yadda aka gano hannun ‘yan kasashen wajen a ayyukan ta’addanci a wuraren da ake hakar ma’adanai ba bisa ka’ida ba, a yanzu gwamnatin tarayya ta umarci ofishoshin jakadancin kasashen waje da ke Nijeriya su sa ido a kan harkokin ‘yan kasashen su. Gargadin yana zuwa ne musamman ganin shi zargin da ake yi zai iya zama barazana ga dangantakar da ke tsakanin Nijeriya da kasashen da ake magana a kai.
Cikin irin wannan gargadin shi ne wanda aka yi a lokacin mulkin tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari a mastayin martani ga kisan masu hakar ma’adanai 12, wadanda ‘yan bindiga suka kashe a kauyen Unguwar Magro da ke karamar hukumar Shiroro ta Jihar Neja.
- Dangote Ya Ceto Nijeriya Daga Durƙushewa – Otedola
- Ambaliyar Ruwa Ta Yi Ajalin Mutane 8 A Borno Da Yobe
Sanarwar daga ofishin Ministan ma’adanai, Dele Alake, ta nuna cewa, lallai a akwai hannun ‘yan kasashen waje a harkokin ta’addancin da ake tafkawa a wuraren hakar ma’adanai ba bisa ka’ida ba, a fadin tarayyar Nijeriya. Sanarwar ta kuma nuna cewa, duk wanda aka kama za a tuhume shi da yi wa kasa zagon kasa.
Wanan jaridar na tunatar da masu karatu cewa a ranar 3 ga watan Yuni 2024, wani wurin hakar ma’adanai ya rushe a karamar hukumar Shiroro ta Jihar Neja, inda ya rushe a kan masu hakar ma’adanai da dama, ya binne su da ran su. Wata kungiya mai zaman kanta mai suna ‘Reneblyn Debelopment Initiatibe (RDI)’ da ke harkokin ta a Jihar Neja, ta bayyaan cewa, a lokacin da ta ziyarci kauyen Galadima-Kogo, inda lamarin ya faru. Kauyawan sun karyata ikirarin hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Jihar inda ta ce, mutum 30 ne suka makale.
Mako 2 kacal dayin hakan wani wurin hakar ma’adanai kuma ya rufta a kauyen Bazakwoi a yankin Adunu da ke karamar hukumar Paikoro duk dai a Jihar Neja, inda aka tabbatar da mutuwar mutum 3 aka kuma samu nasarar ceto mutum 1 da ransa.
Shugaban Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Jihar Neja (NEMA), Alhaji Abdullahi Baba Arah, ya tabbatar da faruwar lamarin, ya kuma kara da cewa, lamarin ya faru ne a wurin hakar gwal ba bisa ka’ida ba inda ya kai ga mutuwar masu hakar ma’adanai 3.
Idan dai za a iya tunawa a shekarar da ta gabata ne a aka haramta harkokin hakar ma’adanai a yankin Shiroro da kewaye saboda rashin ingancin wuraren da ake hakar ma’adanan da hatsarin da ake tattare dayin hakan. Amma kuma tashin hankalin a nan shi ne yadda ake danne rahotannin hadurran da ake samu a wuraren hakar ma’adanai ba bisa ka’ida ba, yawanci ya fi rutsawa da masu hakar ma’adanai ba bisa ka’ida ba ne wadanda ‘yan kasashen waje da masu goya masu baya na cikin gida ke daukar nauyi.
A ‘yan kwanakin nan, an samu karin rahotannin mace-mace masu hakar ma’adanai ba bisa ka’ida ba,ya fi rutsawa da kauyawa marasa aikin yi da suke neman tsira daga matsin tattalin arzikin da ake fuskanta. A watan Janairu na shekarar 2024, mata biyu masu hakar ma’adanai suka mutu a wurin hakar ma’adanai ba bisa ka’ida ba a kauyen Gudum Seyawa, da ke Jihar Bauchi.
Haka kuma a watan Janairu na wannan shekarar an samu fashewar wasu abubuwa a garin Ibadan inda mutum 2 suka mutu yayin da mutum 77 suka samu raunuka daban-daban, an dora alhakin ita fashewar a kan nakiyoyin da masu hakar ma’adanai ba bisa ka’ida ba suka boye.
Masana sun ce, yawaitar hadarorin da ake samu a wuraren hakar ma’adanai ba bisa ka’ida ba, yana nuna mana halin da bangaren hakar ma’adanan ke ciki ne, wadanda suka hada da lalata muhalli, cin zarafin yara da kuma rashin cikakken sa ido daga hukumomin da suka kamata, wanda aikin sune tabbatar da tsaron lafiyar al’ummar da ke mu’amala da wuraren hakar ma’adanai a kasar nan.
Mun damu kwarai da gaske akan yadda gwamatocin tarayya dana jihoji suke nuna halin ko’in kula a kan matsalolin da suka dabaibaye bangaren hakar ma’adanai a kasar nan. Ya kamata gwamanati ta dauki matakai domin magance yadda wuraren hakar ma’adanai ke ruftawa suna kashe mutane da dama da kuma hadurran da suke tattare da hakar ma’adanai a Nijeriya gaba daya.
Bayan matsaloli da suke tattare da masu hakar ma’adanai ba bisa ka’ida ba, akwai kuma rashin daidaita tsakanin gwamanatin tarayya da gwamnatocin jihohi a kan tafiyar da dokokin da suke da alaka da harkar ma’adanai a kasar nan.
A wani taron da aka gudanar a kan lamarin kwanan nan, masu ruwa da tsaki a bangaren sun yi gargadi gwamanati a kan karuwar tashin hankali a bangaren hakar ma’adanai wanda suka ce zai iya kawo cikas, ci gaba bangaren a nan gaba.Sun lura da cewa harkokin wasu gwamnatocin jihohi suna karo da kokarin da gwamnatin tarayya take yi na jawo hankalin masu zuba jari daga kasashen waje yana kuma kawo cikas ga ci gaban masana’antar hakar ma’adanai a kasar baki daya.
Su kuma lura da cewa, katsalandan da gwamatin jihojhi suke yi a harkokin hakar ma’adanai a jihojinsu shi ne babbar matsalar da ci gaban hakar ma’adanai ke fuskanta a Nijeriya, musamman ma in aka lura da tanadin kundin tsarin mulkin kasar nan inda dokar hakar ma’adanai ta kasa (Mining Act of 2007) ta dora wa gwamnatin tarayya gaba daya alhakin mallaka da tafiyar da ma’adanai a Nijeriya.
A ra’ayinmu, ya kamata ma’aikatar ma’adanai ta gaggauta aiwatar da tsare -tsaren kawo gyara a bangaren ma’adanai a kasar nan da nufin samar da gyaran da ake bukata.Hakanan ma akwai bukatar wayar da kan jihohi a kan bukatar su cire hannun su a kan duk abin da ya shafi harkokin ma’adanai kamar yadda dokar ta tanadar.