ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Thursday, June 4, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Mace-mace A Wuraren Hakar Ma’adanai

by Ra'ayinmu
2 years ago

Bayan samun rahotannin mace-macen mutane a wuraren hakar ma’adanai ba bisa kan ka’ida ba da kuma yadda aka gano hannun ‘yan kasashen wajen a ayyukan ta’addanci a wuraren  da ake hakar ma’adanai ba bisa ka’ida ba, a yanzu gwamnatin tarayya ta umarci ofishoshin jakadancin kasashen waje  da ke Nijeriya su sa ido a kan harkokin ‘yan kasashen su. Gargadin yana zuwa ne musamman ganin shi zargin da ake yi zai iya zama barazana ga dangantakar da ke tsakanin Nijeriya da kasashen da ake magana a kai.

Cikin irin wannan gargadin shi ne wanda aka yi a lokacin mulkin tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari a mastayin martani ga kisan masu hakar ma’adanai 12, wadanda ‘yan bindiga suka kashe a kauyen Unguwar Magro da ke karamar hukumar Shiroro ta Jihar Neja.

  • Dangote Ya Ceto Nijeriya Daga Durƙushewa – Otedola
  • Ambaliyar Ruwa Ta Yi Ajalin Mutane 8 A Borno Da Yobe

Sanarwar daga ofishin Ministan ma’adanai, Dele Alake, ta nuna cewa, lallai a akwai hannun ‘yan kasashen waje a harkokin ta’addancin da ake tafkawa a wuraren hakar ma’adanai ba bisa ka’ida ba, a fadin tarayyar Nijeriya. Sanarwar ta kuma nuna cewa, duk wanda aka kama za a tuhume shi da yi wa kasa zagon kasa.

ADVERTISEMENT

Wanan jaridar na tunatar da masu karatu cewa a ranar 3 ga watan Yuni 2024, wani wurin hakar ma’adanai ya rushe a karamar hukumar Shiroro ta Jihar Neja, inda ya rushe a kan masu hakar ma’adanai da dama, ya binne su da ran su. Wata kungiya mai zaman kanta mai suna ‘Reneblyn Debelopment Initiatibe (RDI)’ da ke harkokin ta a Jihar Neja, ta bayyaan cewa, a lokacin da ta ziyarci kauyen Galadima-Kogo, inda lamarin ya faru. Kauyawan sun karyata ikirarin hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Jihar inda ta ce, mutum 30 ne suka makale.

Mako 2 kacal dayin hakan wani wurin hakar ma’adanai kuma ya rufta a kauyen Bazakwoi a yankin Adunu da ke karamar hukumar Paikoro duk dai a Jihar Neja, inda aka tabbatar da mutuwar mutum 3 aka kuma samu nasarar ceto mutum 1 da ransa.

LABARAI MASU NASABA

Mambobin NYSC 4, Soja da Mutum 1 Sun Rasu A Hatsarin Mota A Adamawa

Sarki Sanusi II Ya Tuɓe Rawanin Mai Unguwar Rikadawa Kan Badaƙalar Fili

Shugaban Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Jihar Neja (NEMA), Alhaji Abdullahi Baba Arah, ya tabbatar da faruwar lamarin, ya kuma kara da cewa, lamarin ya faru ne a wurin hakar gwal ba bisa ka’ida ba inda ya kai ga mutuwar masu hakar ma’adanai 3.

Idan dai za a iya tunawa a shekarar da ta gabata ne a aka haramta harkokin hakar ma’adanai a yankin Shiroro da kewaye saboda rashin ingancin wuraren da ake hakar ma’adanan da hatsarin da ake tattare dayin hakan. Amma kuma tashin hankalin a nan shi ne yadda ake danne rahotannin hadurran da ake samu a wuraren hakar ma’adanai ba bisa ka’ida ba, yawanci ya fi rutsawa da masu hakar ma’adanai ba bisa ka’ida ba ne wadanda ‘yan kasashen waje da masu goya masu baya na cikin gida ke daukar nauyi.

A ‘yan kwanakin nan, an samu karin rahotannin mace-mace masu hakar ma’adanai ba bisa ka’ida ba,ya fi rutsawa da kauyawa marasa aikin yi da suke neman tsira daga matsin tattalin arzikin da ake fuskanta. A watan Janairu na shekarar 2024, mata biyu masu hakar ma’adanai suka mutu a wurin hakar ma’adanai ba bisa ka’ida ba a kauyen Gudum Seyawa, da ke Jihar Bauchi.

Haka kuma a watan Janairu na wannan shekarar an samu fashewar wasu abubuwa a garin Ibadan inda mutum 2 suka mutu yayin da mutum 77 suka  samu raunuka daban-daban, an dora alhakin ita fashewar a kan nakiyoyin da masu hakar ma’adanai ba bisa ka’ida ba suka boye.

Masana sun ce, yawaitar hadarorin da ake samu a wuraren hakar ma’adanai ba bisa ka’ida ba, yana nuna mana halin da bangaren hakar ma’adanan ke ciki ne, wadanda suka hada da lalata muhalli, cin zarafin yara da kuma rashin cikakken sa ido daga hukumomin da suka kamata, wanda aikin sune tabbatar da tsaron lafiyar al’ummar da ke mu’amala da wuraren hakar ma’adanai a kasar nan.

Mun damu kwarai da gaske akan yadda gwamatocin tarayya dana jihoji suke nuna halin ko’in kula a kan matsalolin da suka dabaibaye bangaren hakar ma’adanai a kasar nan. Ya kamata gwamanati ta dauki matakai domin magance yadda wuraren hakar ma’adanai ke ruftawa suna kashe mutane da dama da kuma hadurran da suke tattare da hakar ma’adanai a Nijeriya gaba daya.

Bayan matsaloli da suke tattare da masu hakar ma’adanai ba bisa ka’ida ba, akwai kuma rashin daidaita tsakanin gwamanatin tarayya da gwamnatocin jihohi a kan tafiyar da dokokin da suke da alaka da harkar ma’adanai a kasar nan.

A wani taron da aka gudanar a kan lamarin kwanan nan, masu ruwa da tsaki a bangaren sun yi gargadi gwamanati a kan karuwar tashin hankali a bangaren hakar ma’adanai wanda suka ce zai iya kawo cikas, ci gaba bangaren a nan gaba.Sun lura da cewa harkokin wasu gwamnatocin jihohi suna karo da kokarin da gwamnatin tarayya  take yi na jawo hankalin masu zuba jari daga kasashen waje yana kuma kawo cikas ga ci gaban masana’antar hakar ma’adanai a kasar baki daya.

Su kuma lura da cewa, katsalandan da gwamatin jihojhi suke yi a harkokin hakar ma’adanai a jihojinsu shi ne babbar matsalar da ci gaban hakar ma’adanai ke fuskanta a Nijeriya, musamman  ma in aka lura da tanadin kundin tsarin mulkin kasar nan inda dokar hakar ma’adanai ta kasa (Mining Act of 2007) ta dora wa gwamnatin tarayya gaba daya alhakin mallaka da tafiyar da ma’adanai a Nijeriya.

A ra’ayinmu, ya kamata ma’aikatar ma’adanai ta gaggauta aiwatar da tsare -tsaren kawo gyara a bangaren ma’adanai a kasar nan da nufin samar da gyaran da ake bukata.Hakanan ma akwai bukatar wayar da kan jihohi a kan bukatar su cire hannun su a kan duk abin da ya shafi harkokin ma’adanai kamar yadda dokar ta tanadar.

Ma'adanai
Ra'ayinmu
+ postsBio
  • Ra'ayinmu
    https://hausa.leadership.ng/author/raayinmu/
    Shin Nijeriya Ta Shirya Tunkarar Dawowar Annobar Ebola?
  • Ra'ayinmu
    https://hausa.leadership.ng/author/raayinmu/
    Buƙatar Samar Da Alƙibla Ta Musamman Ga Gidajen Gyaran Hali Na Ƙasar Nan
  • Ra'ayinmu
    https://hausa.leadership.ng/author/raayinmu/
    Ce-ce-ku-ce Kan Batun Biyan Bashin Naira Tiriliyan 3.3 Na Kuɗin Lantarki
  • Ra'ayinmu
    https://hausa.leadership.ng/author/raayinmu/
    Matsalar Ɓacewar Gandun Dazukan Nijeriya

MASU ALAKA

Mambobin NYSC 4, Soja da Mutum 1 Sun Rasu A Hatsarin Mota A Adamawa
Labarai

Mambobin NYSC 4, Soja da Mutum 1 Sun Rasu A Hatsarin Mota A Adamawa

June 4, 2026
Sarki Sanusi II Ya Tuɓe Rawanin Mai Unguwar Rikadawa Kan Badaƙalar Fili
Manyan Labarai

Sarki Sanusi II Ya Tuɓe Rawanin Mai Unguwar Rikadawa Kan Badaƙalar Fili

June 4, 2026
Uba Sani Ya Sanya Hannu Kan Sabbin Dokoki A Bangaren Sauya Fannin Wuta, Noma, Da Muhalli
Labarai

Uba Sani Ya Sanya Hannu Kan Sabbin Dokoki A Bangaren Sauya Fannin Wuta, Noma, Da Muhalli

June 3, 2026
Next Post
Karin Kudin Mai: Hakika An Ci Amanarmu, In Ji ‘Yan Kwadago

Tawagar Masanan Dakile Yaduwar Cututtuka Ta Sin Ta Isa DR Congo

Tawagar Masanan Dakile Yaduwar Cututtuka Ta Sin Ta Isa DR Congo

June 3, 2026
Uba Sani Ya Sanya Hannu Kan Sabbin Dokoki A Bangaren Sauya Fannin Wuta, Noma, Da Muhalli

Uba Sani Ya Sanya Hannu Kan Sabbin Dokoki A Bangaren Sauya Fannin Wuta, Noma, Da Muhalli

June 3, 2026
Han Zheng Zai Halarci Taron SPIEF Karo Na 29 A Rasha Tare Da Gudanar Da Ziyarar Aiki A Belarus

Han Zheng Zai Halarci Taron SPIEF Karo Na 29 A Rasha Tare Da Gudanar Da Ziyarar Aiki A Belarus

June 3, 2026
Majalisa Ta Nemi Tinubu Ya Canza Dabarun Yaƙi Da Ta’addanci Don Kawo Ƙarshen Kashe-kashe

’Yan Majalisar Tarayya 3 Sun Fice Daga APC Zuwa ADC da PRP

June 3, 2026
An Fara Watsa Shirye-Shirye Masu Taken “Sha’awar Xi Jinping Ga Al’adu” Da Sauran Fina-Finan Bayyana Labaran Sin A Kasar Laos

An Fara Watsa Shirye-Shirye Masu Taken “Sha’awar Xi Jinping Ga Al’adu” Da Sauran Fina-Finan Bayyana Labaran Sin A Kasar Laos

June 3, 2026
Tambuwal Ya Jajanta Wa Waɗanda Harin ’Yan Bindiga Ya Shafa A Sokoto, Ya Nemi A Ƙara Tsaro

Tambuwal Ya Jajanta Wa Waɗanda Harin ’Yan Bindiga Ya Shafa A Sokoto, Ya Nemi A Ƙara Tsaro

June 3, 2026
Gwamnatin Beijing Ta Amince Da Kafa Cibiyar Kirkire-Kirkiren Fasahar Lissafi Mai Nasaba Da Sararin Samaniya

Gwamnatin Beijing Ta Amince Da Kafa Cibiyar Kirkire-Kirkiren Fasahar Lissafi Mai Nasaba Da Sararin Samaniya

June 3, 2026
Za A Fara Buga Gasar Kofin Sarkin Gombe Bayan Masu Ruwa Da Tsaki Sun Cimma Matsaya

Za A Fara Buga Gasar Kofin Sarkin Gombe Bayan Masu Ruwa Da Tsaki Sun Cimma Matsaya

June 3, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.