• English
  • Business News
Thursday, October 9, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

An Tona Asirin Ainihin Dalilin Saukar Hadimin Tinubu

by Abubakar Sulaiman
1 year ago
Tinubu

Ajuri Ngelale, mai magana da yawun Shugaba Bola Tinubu ya sanar da yin murabus daga muƙaminsa, inda ya bayyana matsalolin lafiyar iyalinsa a matsayin babban dalilin da ya sa zai ɗauki hutu na ɗan lokaci. Sai dai, wasu majiyoyi na nuna cewa akwai wani dalilin ajiye aikin nasa saɓanin yadda aka bayyana.

Rahotanni sun nuna cewa ficewar Ngelale daga fadar shugaban ƙasar ta samo asali ne daga rikice-rikicen cikin gida da rashin jituwa a tsakanin tawagar watsa labaran shugaban ƙasar.

  • Bola Tinubu Da Wasu Shugabannin Afirka Sun Iso Beijing Don Halartar Taron FOCAC
  • Tinubu Ya Yi Ta’aziyyar Rasuwar Hajiya Dada Yar’adua

Ana zargin cewa akwai matsin lamba na a sauya shi da wanda ake ganin yana da kyakkyawar alaka da manema labarai da kuma mafi dacewa da ra’ayin shugaba Tinubu.

Bugu da ƙari, yadda ya ke gudanar da ayyuka daban-daban – daga matsayinsa na mai magana da yawun shugaban ƙasa zuwa mukaman wakilin shugaban ƙasa kan sauyin yanayi da kuma shugaban kwamitin kula da aikin Project Evergreen – ya shafi aikinsa na asali a harkokin watsa labarai.

Rikicin cikin gida da sauran ma’aikatan watsa labarai, tare da yadda tasirinsa ke ƙaruwa a ɓangaren sauyin yanayi, sun ƙara janyo wannan rashin jituwa.

LABARAI MASU NASABA

Da Ɗumi-ɗumi: Tinubu Ya Zaɓi Farfesa Amupitan A Matsayin Sabon Shugaban INEC 

Kotu Ta Ba Da Umarnin Kama Tsohon Shugaban INEC, Mahmood Yakubu, Kan Saɓa Umarninta

Lamarin ya kai ga an umarce shi ya zaɓi tsakanin ci gaba da zama mai magana da yawun shugaban ƙasa ko kuma mayar da hankali kan aikin sa na sauyin yanayi. Da ya zaɓi ci gaba da mukaminsa na mai magana da yawun shugaban ƙasa, an zargi wasu daga cikin manyan na kusa da shugaban ƙasa da yin katsalandan, wanda hakan ya janyo ajiye  dukkan mukaman nasa.

Wasu majiyoyi sun nuna cewa shugaba Tinubu na iya naɗa tsohon Shugaban Ma’aikatansa, Sunday Dare, a matsayin wanda zai maye gurbin Ngelale, duk da cewa ba a tabbatar da wannan ba.

Ngelale bai ce komai ba a fili game da wannan batu, kuma duk wani ƙoƙari na samun karin bayani daga gare shi ya ci tura kamar yadda jaridar Daily Nigerian ta rawaito.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Da Ɗumi-ɗumi: Tinubu Ya Zaɓi Farfesa Amupitan A Matsayin Sabon Shugaban INEC 
Manyan Labarai

Da Ɗumi-ɗumi: Tinubu Ya Zaɓi Farfesa Amupitan A Matsayin Sabon Shugaban INEC 

October 9, 2025
Kotu Ta Ba Da Umarnin Kama Tsohon Shugaban INEC, Mahmood Yakubu, Kan Saɓa Umarninta
Manyan Labarai

Kotu Ta Ba Da Umarnin Kama Tsohon Shugaban INEC, Mahmood Yakubu, Kan Saɓa Umarninta

October 9, 2025
Gobara Ta Sake Ƙone Kasuwar Oba A Benin
Manyan Labarai

Gobara Ta Sake Ƙone Kasuwar Oba A Benin

October 9, 2025
Next Post
Fadawa Soyayya Saboda Tausayin Budurwa Da Yadda Abin Ke Sauyawa

Fadawa Soyayya Saboda Tausayin Budurwa Da Yadda Abin Ke Sauyawa

LABARAI MASU NASABA

Da Ɗumi-ɗumi: Tinubu Ya Zaɓi Farfesa Amupitan A Matsayin Sabon Shugaban INEC 

Da Ɗumi-ɗumi: Tinubu Ya Zaɓi Farfesa Amupitan A Matsayin Sabon Shugaban INEC 

October 9, 2025
Adadin Biyan Kudade Ta Intanet Yayin Hutun Bikin Kafuwar Jamhuriyar Jama’ar Sin Ya Kai Yuan Tiriliyan 13.26

Adadin Biyan Kudade Ta Intanet Yayin Hutun Bikin Kafuwar Jamhuriyar Jama’ar Sin Ya Kai Yuan Tiriliyan 13.26

October 9, 2025
SSANU Da NASU Sun Yi Zanga-Zanga A Abuja Kan Rashin Cika Alƙawarin Gwamnati

SSANU Da NASU Sun Yi Zanga-Zanga A Abuja Kan Rashin Cika Alƙawarin Gwamnati

October 9, 2025
An Umurci Manyan Makarantu Su Mayar Da Kuɗaɗen TETFund Da Ba Su Kashe Ba

An Umurci Manyan Makarantu Su Mayar Da Kuɗaɗen TETFund Da Ba Su Kashe Ba

October 9, 2025
Kotu Ta Ba Da Umarnin Kama Tsohon Shugaban INEC, Mahmood Yakubu, Kan Saɓa Umarninta

Kotu Ta Ba Da Umarnin Kama Tsohon Shugaban INEC, Mahmood Yakubu, Kan Saɓa Umarninta

October 9, 2025
Gobara Ta Sake Ƙone Kasuwar Oba A Benin

Gobara Ta Sake Ƙone Kasuwar Oba A Benin

October 9, 2025
Kofin Duniya U-20: Argentina Ta Lallasa Nijeriya Da Ci 4-0

Kofin Duniya U-20: Argentina Ta Lallasa Nijeriya Da Ci 4-0

October 9, 2025
Ni Ne Ɗan Siyasa Mafi Shahara A Kudu Maso Gabas, Ba Peter Obi Ba – Orji Kalu

Ni Ne Ɗan Siyasa Mafi Shahara A Kudu Maso Gabas, Ba Peter Obi Ba – Orji Kalu

October 9, 2025
HOTUNA: Yadda Obasanjo Ya Ƙaddamar Da Sabuwar Cibiyar Taron Ƙasa Da Ƙasa A Bauchi

HOTUNA: Yadda Obasanjo Ya Ƙaddamar Da Sabuwar Cibiyar Taron Ƙasa Da Ƙasa A Bauchi

October 9, 2025
Tattalin Arziƙin Nijeriya Ya Ƙaru Da Kashi 3.9 – Bankin Duniya

Tattalin Arziƙin Nijeriya Ya Ƙaru Da Kashi 3.9 – Bankin Duniya

October 9, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.