Kisan da aka yi wa Alhaji Isa Muhammad Bawa, Sarkin Gobir na Gatawa da ke Jihar Sakkwato kwanannan ya kara fito da tsanannin matsalar tsaro a Nijeriya. Lamarin da ya faru a ranar 21 ga watan Agusta 2024 ya tayar da hankali matuka a kan tsaron lafiyar Sarakunan gargajiya a Nijeriya da ma sauran ‘yan Nijeriya gaba daya ya kuma fito da iri hali da iya aiki ko akasinsa na jami’an tsaron mu.
Kasancewar Sarkin Gobir Bawa da dansa sun kasannce a hannu ‘yan ta’adda na kusan wata daya kafin su kashe shi, duk kuwa da kokarin ceto shi da aka yi ya nuna sakaci da rashin iya aiki na masu tafiyar da harkokin tsaron kasar nan a wannan irin halin tabarbarewar tsaron da ake ciki.
- ‘Yan Bindiga Sun Sace Matafiya A Babbar Hanyar Gusau-Funtua
- Kotu Ta Bada Belin Masu Zanga-Zangar Tsadar Rayuwa Kan Naira Milyan 10 Kowanensu
An kama Sarkin Gobir Bawa ne a ranar 27 ga watan Yuli,2024, tare da dansa, Kabiru Isa, yayin da suke dawowa daga taro a fadar Sarkin Musulmi da aka yi Sakkwato. Duk kokarin da iyalansa da masarautar Gobir ta yi ga gwamatin Jihar har ma da sakon bidiyon da aka turo daga mabuyar ‘yan ta’adda hakan bai wani taimaka ba. Lokacin da aka kai kudin fansa na naira Miliyan 60 da ‘yan ta’addan suka nema lokaci ya kure domin sun dade da kashe shi inda daga baya suka sako dansa.
Bayan mutuwarsa, kamar dai kowane lokaci sai ihun tir da kisan ke fitowa daga dukkan bangarori, inda gwamati ta sha alwashin kamo wadanda suka yi kisan. Wannan bai isa ba domi tamkar shan magani ne bayan mutuwa ne, ya kamata a ce jamai’an tsaro sun bi sawun masu garkuwa kamar yadda suka bi sawun wadanda suka sace dalibai likitoci na jami’ar Benuwai.Muna jinjina ga kokarin al’umma yankin maza da mata da suka fatattaki ‘yan ta’adda inda suka kwato gawar marigayi Sarkin suka kuma kwato wasu da aka yi garkuwa da su. Wannan abin da ya faru da a wasu kasashe ne da lallai an hukunta wasu daga cikin jami’an tsaron da ke da alhakin tabbatar da tsaro a yankin.
A watan Mayun 2024, ‘yan bindiga sun kashe Chif Auwal Wali, Sarkin gargajiya na Gidan Usmanu da ke Jihar Taraba.Hakanan kuma a watan Yuli ‘yan bindiga sun yi wa Sarkin Takum, Tanimu Kunbiya da dansa kwantan bauna yayin da suke dawowa daga wata jana’iza a jihar Taraba.
A watan Agusta 2024, Sarakunan gargajiya da Sarakunan kauyuka 6 a garin Umucheke Okwe da ke karamar hukumar Onuimo na Jihar Imo aka kashe yayin da suke gudanar da wani taron neman zaman lafiya. Haka kuma a watan Yuli na shekarar data gabata an kashe sarakunan gargajiya da dama ciki har da na Nguru da ke karamar hukumar Aboh Mbaise,Eze Mmirioma, da Eze Joe-Benz Ochulor, Olu 1 na Otulu Amumara na masarautar Ezinihitte Mbaise da ke Jihar Imo.
A farkon watan Agusta, ‘yan bindiga sun kashe basaraken Umuihe da ke Jihar Ebonyi State, mai martaba Umazi Ibo Ubani.
A watan Disamba na shekarar 2023, ‘yan ta’adda sun kashe hakimin Yankuzo, Alhaji Hamza Kogo, da ke masarautar Tsafe a Jihar Zamfara a lokacin da suka yi kokarin yin garkuwa da shi da iyalansa.Haka kuma a shekarar 2020 aka kashe basaraken Olufon na Ifon, Oba Israel Adeusi, a kan babbar hanyar Ifonzuwa Benin a daidai watan Nuwamba na shekarar 2020.An dade ana aikata ta’addanci a kan Sarakunan gargajiya, rahotannin sun nuna cewa, an kashe fiye da sarakuna gargajiya 53 a cikn shekara 10 da suka wuce, kamar dai yadda rahoton wata kungiya mai zaman kanta mai suna SMB 2021 ta ruwaito.
Ya kamata a kawo karshen ta’addanci a kan Sarakunan gargajiya.Dole ne gwamati da jami’an tsaro su samar da yanayi na tsaro ga Sarakunan gargajiya da ‘yan kasa baki daya. Wannan kuma ba yana nufin samar masu jami’an tsaro masu kare lafiyarsu kadai ba, harma da samar da hanyoyin tattara bayanan sirri domin katse kokari da shirin ‘yan ta’adda na kai hari da sace Sarakunan gargajiya a sassan Nijeriya.
Karfafa hanyoyin tsaro a tsakanin al’umma zai taimaka wajen tabbatar da tsaro da kuma kawo karshen harkokin ‘yan ta’adda da ta’addanci a kasa, zai kuma taimaka wajen kawo karshen yadda ake sace Sarakunan gargajiya a kasar nan.
Wani rahoto da bincikenh da aka gudanar kwanan nan ya nuna yadda aka biya fiye da naira biliyan 1 a matsayin kudin fansa a tsakanin watan Yuli na shekarar 2023 zuwa watan Yuni na shekara 2024. Wadannan kudin hana shigewa ne ta hanyar bankuna. Ya kamata ayi amfani da hanyoyi na zamani wajen bin sawun kudaden tare da kama ‘yan ta’addar da masu daukar nauyinsu.
Ya kuma kamata Nijeriya ta hada kai da kwararru daga kasashen waje wajen yaki da harkokin ta’addanci da ‘yan ta’adda musamman ma ganin matsalolin tsaron da ake fuskanta a kasar nan suna da yawan gaske.
Kisan Sarkin Gobir Bawa da yadda ayyukan ta’addanci ke kara karuwa yana nuna raunin masu tafiyar da harkokin gwamanti a kasar nan.
A yayin da muke alhinin kashe-kashen da ake yi mana, ya kamata mu hada karfi da karfe wajen kawo karshen ayyukan ‘yan ta’adda da ta’addanci a sassan kasar nan musamman ma yadda ake ci wa Sarakunan gargajiyar mutunci wadanda sune ke dauke da mutuncin mu da al’adun mu.