Ballewar Madatsar Ruwan Alau da ke karamar hukumar Konduga ta Jihar Borno ta jawo mummunan ambaliyar ruwan da ta mamaye gidajen jama’a tare da haifar da asarar dukiya mai dimbin yawa a Maiduguri, babban birnin Jihar Borno.
Haka zalika ambaliyar ta malale gidan ajiye namun daji (Zoo), wanda hakan ya jawo namun dajin fantsama cikin gari, wasu kuma suka mutu a ruwa.
- ‘Yan Bindiga Sun Sace Matafiya A Babbar Hanyar Gusau-Funtua
- Kasar Sin Za Ta Zurfafa Hadin Gwiwa Da Sauran Kasashe A Bangaren Tsaron Intanet
A ranar Litinin gwamnatin jihar ta gargadi mazauna unguwanni masu makwabtaka da Gidan Namun Dajin da ke unguwar Sanda Kyarimi su gaggauta ficewa daga gidanjensu domin kauce wa hatsarin farmakin dabbobin.
Jama’a da dama a birnin Maiduguri sun tabbatar wa da LEADERSHIP Hausa cewa ambaliyar ruwan ta nutsar da gidajensu tare da ofisoshin gwamnati. Haka nan ruwan bai kyale fadar Shehun Borno ba tare da sauran muhimman wurare na birnin.
Bugu da kari, al’ummar da ke zaune a wasu unguwannin birnin Maiduguri sun bayyana karin fargabar irin yadda namun dajin suka fantsama cikin garin; wadanda suka hada da macizai, kadoji, mugun dawa, da sauran dabbobin masu hatsari.
Wasu bayanai sun bayyana fargabar cewa ambaliyar ruwan ta kashe wasu da dama daga cikin dabbobin, irin su zakunan da suka tsufa kana wasu zakunan tare da jiminai sun tsere, duk da har zuwa lokacin hada wannan rahoto ba a samu wani rahoto na ta’asar da namun dajin da suka tsere suka yi wa al’ummar birnin ba.
Ambaliyar ta fara ce tun daga karshen mako kadan-kadan kafin daga bisani ta yi kamari a ranar Talata biyo bayan fashewar Madatsar Ruwan ta Alau. Unguwannin da al’amarin ya fi shafa sun hada da Fori, Galtimari, Gwange, Bulabulin, da tashar Bama.
Sauran unguwannin da ambaliyar ta malale a birnin na Maiduguri sun hada da London Ciki, Gidan Danbe, Zara Plaza, Lagos Street, Abbaganaram, Kofa, Budum, Kalari, Shehuri, Shehuri North, da kuma Post Office na Rukunin Gidajen Dikwa.
Har ila yau, ambaliyar ta mamaye gidaje, manyan hanyoyin mota da gadoji wanda kawo lokacin hada wannan rahoto ba a iya kiyasta yawan gidanjen da abin ya shafa ba, ballantana asarar da ta jawo.
Wasu rahotanni daga kafafen yada labarai daban-daban sun bayyana cewa akalla mutune 200,000 zuwa 500,000 ambaliyar ta shafa. Tarihi ya nuna cewa an taba yin makamanciyar ta kimanin shekaru 30 da suka gabata, a watan Satumbar 1994, a daidai irin wannan lokacin na bana, duk dai a sanadiyyar ballewar madatsar ruwan ta Alau.
Sai dai barnar da ake ganin ambaliyar wannan karon ta haifar ta dara ta wancan karon.
A cikin wata sanarwa da Gwamnatin Jihar Borno ta fitar, mai dauke da sa hannun Kwamishinan Yada Labaru da Al’amurran Cikin Gida, Farfesa Usman Tar, da safiyar ranar Talata, gwamnatin ta gargadi mazauna wasu unguwanni a birnin na Maiduguri su gaggauta kaurace wa yankunan da ambaliyar ta shafa.
“Saboda kwararowar ruwan ta saba da yadda aka saba, muna kira ga daukacin jama’ar da ke zaune a wuraren da ambaliyar ke yin barazana, a matsayin matakin kare rayukan al’umma da dukiyoyinsu cikin gaggawa, su kaurace wa wuraren da abin ya shafa.
“Har ila yau mun dauki wannan matakin ne bisa ga bayanan da muka samu na fashewar Madatsar Ruwan Alau, kuma ya tunkaro cikin gari, baya ga lalata gonaki da ya yi.” In ji sanarwar.
Tuni dai gwamatin tarayya ta mika sakon jaje ga al’ummar Jihar Borno a kan faruwar wannan ibtila’in, inda mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima ya kai ziyarar gani ido sassan da abin ya shafa.
Da yake jawabi a wani matsugunin mutanen da abin ya shafa, Shettima ya ce, gwamnati ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen aiko da dukkan taimakon da ake bukata na ragewa al’umma radadin da suke fuskanta. Ya kuma yaba wa kokari Gwamna Zulum a kan yadda ya dauki matakin gaggawa wajen tura hukumomin bayar da agaji na jihar wuraren da ake bukatar taimako.
Gwamatin jihar dai ta ayyana cewa, fiye da kashi 80 na al’ummar jiihar ambaliyar ta shafa, ta kuma ce, bukaci jama’a sus a ido tare da kula da sosai wajen kiyaye lafiyarsu musamman bisa silalewar namun daji zuwa cikin gari.
Ambaliyar dai ta tilasta rufe muhimman wurare a jihar da suka hada da Jami’ar Maiduguri, da kuma wata cibiyar koyar da matasa da ke kusa da Jami’ar. A wata sanarwa da magatakardar Jami’ar, Fatima Muhammad Audu, ta fitar, ta ce an yi haka ne domin kare rayukan dalibai da ma’aikata musanmma ganin ana iya samun barkewar cututtuka da sauran matsaloli skamakom wannan ambaliyar, “Kuma ba ma son a samu wata mastalar da za ta fi karfimu a nan gaba, ana sa ran sake bude makaratar ne a ranar 16 ga watan Satumba 2024 in Allah ya yarda’ in ji ta.
Haka kuma gwamatin JIhar ta umarci a kulle dukkan makarantun gwamnati da na masu zama kansu a fadin jihar har zuwa ranar 23 ga watan Satumba 2024 saboda wanan ibtila’in ambaliyar da aka fuskanta.
Da yake tofa albarkacin bakinsa, shugaban wata kungiya mai zama kanta a Jihar Borno mai suna Network of Cibil Society Organisations’ Kwamrade Bulama Abiso, ya nemi a tabbatar da samar da tallafi issashe ga wadanda ibtila’in ya shafa, domin a cewarsa, iyalai da dama musamman mata da kananan yara sun shiga halin ni’yasu sakamakon ambaliyar.
A halin da ake ciki dai tuni, Gwamatin Jihar Boro ta bude sansanin ‘yan gudun hijira na Bakassi da ke Maiduguri domin tsugunar da wadanda ambaliyar ta shafa.
Hukumar bayar da agajin gaggawa ta kasa (NEMA) ta bayyana cewa, ambaliyar ruwan da ta auku a baya-bayan nan a fadin Tarayyar Nijeriya kafin wannan ta Maiduguri, ta lalata amfanin gona kimanin fadin kadada 16,488 a fadin jihohi 27. Bugu da kari, sama da gidaje 32,000 ne al’amarin ya shafa tare da jefa sama da mutum 227,000 cikin mawuyacin hali.
A nashi bangare, karamin ministan noma da bunkasa abinci a Nijeriya, Sanata Abdullahi Sabi Aliyu, ya bayyana cewa kusan kashi 51 cikin dari na amfanin gona a fadin Nijeriya na fuskantar barazanar ambaliya a 2024. A daya bangaren kuma, ministan ya yi gargadin cewa ambaliyar da ke ci gaba da gudana, za ta kawo babbar cikas da kuma gibi ga kokarin samar da abinci a kasar nan.
Mutanen garin Maiduguri da ambaliyar ruwa ta tarwatsa su bayan da dam din Alau ya fashe a halin yaznu sun fara komawa gidajen su bayan da ruwan ya fara janyewa a hankali a wasu wuraren.
Rahoton kamfanin dillancin labarann Nijeriya ya nuna cewa, mutanenn da suka kwana a waje duk sun kosa su koma gidajen su domin ganin irin barnar da ambaliyar ta yi musu.
Wuraren da ruwan ya fara lafawa sune, Gwange da Gomari. Amma kuma wasu wurare da dama duk ruwa ya mamaye su, al’umma ba za su iya shiga ba a yanzu.
A halin yanzu kugiyar majalisar dinki duniya masu kula da bayar da agaji ta ce, fiye da mutum 239,000 ambaliyar ruwan ta shafa a ganin Maidugri. Mutum 50,000 sun samu mafaka a sansanin ‘ya gudun hijira na Muna.
Ambaliyar ruwa ta haifar da cikas ga samar da wutar latarki da ruwa famfo a sasan garin.