Mai Martaba Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar ya bukaci al’umman kasar nan da a dage da yin addu’o’i domin Allah ya kawo mana karshen matslolin rashin tsaro da ta addabi Nijeriya.
Sarkin Musulmi ya ce rashin tsaro ya zama babban kalubale ko ta’ina a fadin Nijeriya. Ya ce Musulmai da Kirista, manyan da yara a dage da addu’o’i, domin babu abin da ya gagari Allah.
- Xi Ya Taya Tebboune Murnar Sake Zama Shugaban Algeria
- Gwamnatin Tarayya Ta Jajanta Wa Al’ummar Borno Kan Ambaliyar Ruwa
Alhaji Sa’ad ya bayyana haka ne wajen taron bikin murnar Sarkin Doma da ya cika shekaru 20 bisa kujerar sarauta a Jihar Nasarawa.
Haka zalika, Sarkin Musulmi ya bayyana matsalar tabarbarewar tattalin arziki da yanzu al’umma ke fama da mawuyacin kuncin rayuwa a kasan nan. Ya ce matukar aka ci gaba da gaya wa Allah, to zai kawo mana mafita.
Alhaji Sa’ad ya misalta Sarkin Doma, Alhaji Ahmadu Aliyu Onawo a matsayin jarumin sarki da yake da hikima da dabara wajen tafiyar da al’umma.
Ya ce Sarkin ya hada kan al’umman yankin Doma waje guda ba tare da la’akari da nuna bambanci addini ko na kabila ko bangaranci ba. Ya ce kamanta gaskiya da adalci wajen hada kan al’umman Doma.
Sarkin Musulmi ya bukaci masu rike da madafun iko a kasan nan su rika kamanta gaskiya da nuna adalci a ko’ina.
Shi ma Gwamnan Jihar Nasarawa, Injiniya Abdullahi Sule ya ce gwamnatinsa za ta ci gaba da yin aiki kafada da kafada da sarakunan gargajiya domin samun dauwamamen zaman lafiya a fadin Jihar Nasarawa.
Ya ce tabbas hada kai da sarakunan gargajiya yana kara tabbatar da hadin kai da tsaron rayuka da fahintar juna tsakanin al’umman da ke rayuwa a biranai da karkara.
Gwamnan wanda ya samu wakilcin mataimakinsa, Dakta Emmanuel Agwado Akabe, ya bayyana ci gaban a fannin zaman lafiya da aka samu ta albarkacin hada karfi da sarakunan jihar.