A ranar Asabar da ta gabata ne, jirgin kwale-kwale ya nitse da manoma a gwadaben bakin kasuwar da ke Karamar Hukumar Gummi ta Jihar Zamfara.
An samu sabanin alkaluma na adadin wadanda suka rasa rayukansu; sakamakon taho mu gamu da kwale-kwalen ya yi da wani kwale-kwalen dauke da fasinjoji a ciki, wasu kafafen yada labarai sun bayyana cewa, sama da mutum 46 ne suka rasu.
- Sin Ta Harba Tagwayen Taurarin Dan Adam Na Tsarin BeiDou
- Kwangilar Biliyan 30: PDP Ta Bukaci EFCC Ta Binciki Gwamnatin Sakkwato
Wannan dalili ne yasa, Fadar Shugaban Kasa da Ofishin Gwamnan Jihar Zamfara, suka fitar da sanarwar jaje tare da yin ta’aziya ga iyalan wadanda suka rasa rayukansu da sauran al’ummar Zamfara da kasa baki-daya.
Guda daga cikin fasinjojin da tsira daga hatsarin da kwale-kwalen ya yi, Abubakar Danjuma; ya shaida wa wakilinmu yadda abin ya faru da kuma yadda Allah ya tseratar da shi, inda yake cewa; “Muna cikin kwale-kwalen, bayan mun kai tsakiyar ruwa; sai ga wani kwale-kwalen daga inda muka dosa ya kunno kai kawai ya bangaji namu kwale-kwalen; inda nan take igiyarsa ta katse.
Daga nan ne kuma, sai kawai kwale-kwalen namu ya fara tangal-tangal ruwa ya fara shiga ciki, sai ya rika yin kasa ruwa na ci gaba da shiga cikin nasa. Saboda haka, kafin zuwa wani dan lokaci; mun nitse a cikin ruwa, amma cikin ikon Allah da yake wasu daga cikinmu mun iya ruwa; sai Allah ya tseratar da rayukanmu, aka kuma samu nasarar ceto wasu daga ciki. Saboda haka, muna yi wa Allah godiya da ya kubutar da mu”, in ji Danjuma.
Shi kuwa, wanda ya rasa dansa; Malam Ibrahim ya bayyana cewa, haka Allah ya rubuta wa dana Muhammad cewa, a hadarin kwale-kwalen zai rasu; shi yasa ya amshi bawan nasa. Don haka, babu abin da zance da wuce Allah ya ji kansa tare da sauran wadanda suka rasu.
A nata banganen kuwa, Gwamnatin Jihar Zamfara; karkashin jagorancin Gwamna Dauda Lawal, ta bai wa iyalan mamatan tallafin Naira miliyan ashirin.
Mataimakin Gwamnan Jihar, Malam Mani Mummuni ne ya bayyana haka, a lokacin ziyarar ta’aziya ga iyalan mamatan a Fadar Mai Martaba, Sarkin Mafaran Gummi, mai shari’a Hassan Lawal.
Mataimakin, ya kuma bayyana bakincikinsa ga iyalan wadanda suka rasu tare kuma da jajanta wa ‘yan’uwa da abokan arziki.
“Yanzu haka, mun bai wa kwamitin rabon tallafin agajin gaggawa wanda gwamnati ta kafa, karkashin jagorancin Alhaji Salihu mai buhu Gummi, wannan tallafi na Naira miliyan ashirin da za a raba wa iyalan wadanda iftila’in ya shafa.
“Haka zalika, gwamna yana tare da Shugabannin Hukumomin ba da agajin gaggawa da kuma hukumomin da abin ya shafa a kan matsalar madatsun ruwa, don gano matsalar da ke haifar da wadannan hadarurruka; domin kaucewa sake afkuwarsa a nan gaba,” in ji Mataimakin Gwamnan.
Haka zalika, Mataimakin Gwamnan; ya bayar da tabbacin cewa, dukkanin gwadaben da ake amfani da shi wajen tsallake ruwa, babu shakka gwamati za ta yi iya kokarinta na ganin ta samar da mafita.
Mai Martaba Sarkin Mafaran Gummi, Mai Shari’a Hassan Lawal; ya bayyana godiyarsa ga Gwamnatin Jihar Zamfara, kan ta’aziya da kuma tallafin kudi na Naira miliyan ashirin ga iyalan wadannan mamata.
Sarkin, ya kuma tabbatar da cewa; mutane goma ne kadai suka rasa rayukansu, ba arba’in ba kamar yadda wasu kafafen yada labarai suka bayyana. Kazalika, nan take ya bayyana sunayensu a gaban mahaifansu a cikin fadar tasa.
Sarkin Mafaran, ya kuma tabbatar wa da Mataimakin Gwamnan cewa; ya gayyato kungiyar masu kula da kwale-kwalen Jihar Kogi, don neman shawara a kan yadda za a magance matsalar asarar rayuka; sun kuma ba da tasu shawarar za kuma a mika zuwa ga gwamnati, domin shawo kan matsalar.
Shi ma a nasa jawabin, Shugaban Karamar Hukumar Gummi, Nuhu Falale ya bayyana cewa, kin bin doka ga shugabannin masu kulawa da kwale-kwalen, ke haifar da asarar rayukan al’umma.
A karshe, Falale ya yi kira ga gwamnatin jihar; ta taimaka wajen sama musu kwale-kwalen zamani, wanda za su rika amfani da shi wajen jigilar al’ummarsu, domin kaucewa asarar rayuka.