A yau, muna tare da kwararriyar likitar mata; Dakta Hauwa Abdullahi, wadda ta warware zare da abawa a kan dashen da a mahaifar mace; musamman ga wadanda ba za su iya haihuwa da kansu ba.
A cikin mutane, akwai wadanda sukan samu wannan matsala; ko dai ta bangaren maza ko kuma a bangaren matan. Idan ta bangaren mazan ne, akwai yiwuwar ba su da halittun haihuwa; tun fil azal ba a haife su da su ba, wasu kuma an hife da su; daga bisani sai wata matsala ta faru da su a rayuwa, watakila ma sun taba haihuwa a baya.
- Yadda Shugabanni Suka Taya Al’ummar Musulmi Murnar Maulidin Bana
- Bangaren Sin Ya Yi Kira Ga Bangarori Biyu Dake Rikici A Sudan Da Su Yayyafawa Rikicin Kasar Ruwa
Sannan kuma, a bangaren matan su ma a kan samu wadanda bututun haihuwarsu ya toshe ko suka samu matsala ta mahaifa, wadda ba za ta ba su damar iya samun juna biyu da kansu ba. Irin wadanan su ne wadanda ake cewa; sai an yi musu wannan dashe.
Wannan dashe, na nufin a dauki kwan mace; amma wanda ya nuna a hada da kwan namiji su haifar da jariri; sai a mayar da shi cikin mahaifar mace, idan Allah ya amsa; sai ya ci gaba da rayuwa.
A cewar daktar, su ne suka fara wannan dashen da a Jihar Kano, wanda Allah cikin ikonsa; ya kaddara yara da dama a halin yanzu, wadanda aka samu ta hanyar wannan dashe na nan suna ci gaba da rayuwarsu cikin koshin lafiya.
Dakta Hauwa ta kara da cewa, ganin irin wahala da kashe makudan kudade da ake yi ta hanyar fita zuw wasu jihohi ko kasashe, yasa suka jajirce wajen ganin an samu wannan nasara ta fara yin wannan dashe; ga shi kuma cikin ikon Allah abubuwan sun kankama.
“Dalilin harka da masu ire-iren wannan matsala, yasa na san abubuwa da dama game da su; wasu na zuwa wasu jihohi tare da kashe miliyoyi, kafin a kai karshe kuma wasu kudadensu sun kare ba tare da sun samu biyan bukatarsu ba; wannan na daya daga cikin dalilan da suka sa na dage har aka kai ga kafa wannan cibiya”, in ji daktar Hauwa.