Yayin da ci gaba da tattara sakamakon zaɓen gwamna na jihar Edo ke gudana, ɗan takarar mataimakin gwamna na jam’iyyar Labour Party (LP), Asamah Kadiri SAN, ya sha kaye a mazaɓarsa a hannun jam’iyyar APC.
Sakamakon da aka tattara daga wurin zaɓen ya nuna cewa ɗan takarar na LP bai samu nasara ba a mazaɓarsa ta 1, akwati mai lamba ta 6 dake Auchi, a ƙaramar hukumar Etsako ta yamma, inda ya samu ƙuri’u 25 kacal, yayin da jam’iyyun PDP da APC suka samu ƙuri’u 13 da 100.
- Kotu Ta Umarci INEC Ta Tuhumi Gwamnoni Kan Rikice-rikicen Zaben 2023
- Mutum 2,629,025 Ke Da Wuƙa Da Namar Zabo Sabon Gwamnan Edo -INEC
Jaridar LEADERSHIP ta ruwaito cewa Kadiri ya zargi jam’iyyar adawa ta APC da sayen ƙuri’u bayan ya kaɗa ƙuri’arsa a yau Asabar.
Dangane da sakamakon zaɓen, masana sun bayyana cewa ɗan takarar mataimakin gwamna na LP, wanda ya fito daga gidan sarautar Auchi, ba shi da tasiri a siyasar Etsako a yankin mazabar Edo ta Arewa, inda Sanata Adams Oshiomhole ke jagorantar lamuran siyasa.