‘Yar takarar gwamnan jihar Adamawa a karkashin jam’iyyar APC a zaben 2023, Sanata Aisha Dahiru Binani, ta bayar da gudummawar Naira miliyan 50 ga wadanda ambaliyar ruwa ta shafa a garuruwan Maiduguri da Jere a jihar Borno.
Ta bayar da wannan gudummawar ne a ranar Talata a lokacin da ta jagoranci tawagar shugabannin jam’iyyar da magoya bayanta a ziyarar jajen da suka kai wa Gwamna Babagana Zulum, a Maiduguri.
- Jami’an ‘Yansanda 5 Sun Mutu, 11 Sun Jikkata Sakamakon Hatsarin Mota A Kano
- Kasar Sin Ta Lashi Takobin Karfafa Hidimomin Kula Da Tsoffi
Binani wacce ta bayyana Maiduguri a matsayin gida, ta ce, alaka da mutuntaka ne ya sa, su ka zo da jikinsu domin jajanta wa gwamna da al’ummar jihar.
“Muna addu’ar kada irin wannan bala’i ya sake afkawa kowa a duk inda muke. Duk mun sani a tarihi cewa, al’ummar jihar Borno suna da karfin juriya. Muna rokon Allah Madaukakin Sarki da ya kara musu juriya kan wannan musiba kuma ya dauke ta cikin gaggawa.
“Muna kuma addu’ar Allah ya jikan wadanda suka rasa rayukansu, ya ba su Aljannar firdaus, ya kuma bai wa iyalansu da ‘yan uwansu hakuri da juriyar rashin,” inji ta.
Tawagar ta hada da Ambasada, Fatima Balla Abubakar, Sanata Ahmed Hassan Barata da sauran fitattun ‘yan jam’iyyar.
Da yake mayar da martani, Gwamna Zulum ya godewa Sanata Binani da ta zo Maiduguri duk da rashin kyawun yanayi da ya hana ta sauka a ranar Litinin.