• English
  • Business News
Thursday, August 28, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Katsina Za Ta Gudanar Da Jarabawar Tantancewa Ga Shugabanni Da Malaman Sakandire

by Sulaiman
11 months ago
in Manyan Labarai
0
katsina
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

Gwamnatin jihar Katsina ta bayyana shirinta na gudanar da jarabawar tantancewa ga dukkan shugabanni da mataimakan shugabanni, da malaman makarantun sakandire na jihar.

Za a shirya jarrabawar ne da nufin taimaka wa gwamnati wajen sake nada mukamai da kuma tabbatar da matakin da ya dace ga shugabancin makarantu, da inganta kwazo da ingantaccen jagoranci a makarantu.

  • Yawan Jarin Waje Na Kai Tsaye Da Sin Ta Zuba A Bara Ya Kai Dala Biliyan 177.29
  • Jami’an ‘Yansanda 5 Sun Mutu, 11 Sun Jikkata Sakamakon Hatsarin Mota A Kano

Kwamishiniyar ilimin farko da sakandire a jihar, Zainab Musawa ce ta bayyana hakan a Katsina yayin da take yi wa manema labarai karin haske kan yadda daliban jihar suka samu sakamako mai kyau bayan kammala jarabawar kammala sakandire ta kasa (NECO) na shekarar 2024.

Labarai Masu Nasaba

Yadda Aka Cafke Masu Saka Ƙwayoyi A Jakunkunan Matafiya A Filin Jirgin Sama A Kano

Gwamnatin Imo Ta Amince Da N104,000 A Matsayin Sabon Mafi Ƙarancin Albashin Ma’aikata 

Musawa ta bayyana cewa, ma’aikatar ta kuma shirya sake dawo da azuzuwan bada horo na tilas ga duk daliban da suka kusa kammala makarantar sakandire domin kara musu kaimi musamman a fannin Lissafi da Turanci.

Yayin da take jaddada kwazon dalibai a jarabawar NECO, kwamishiniyar ta ce, jihar ta zo ta shida a yawan daliban da suka fita da (credit 5) zuwa sama da haka, da suka hada da Lissafi da Ingilishi, wanda ta bayyana a matsayin babban nasara.

Ta kara da cewa, wannan gagarumar nasara da daliban suka yi, nuni ne na gaskiya da irin jajircewar da gwamnati ta yi wajen kawo sauyi a fannin ilimi, da samar da kayayyakin koyarwa, da kayayyakin aiki, da kuma daukar fiye da malamai 7,000 aiki tun lokacin da gwamnati mai ci a jihar ta zo.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

ShareTweetSendShare
Previous Post

Hadimin Tinubu Ya Raba Kayayyakin Makaranta Ga Daliban Firamare A Kano

Next Post

Kotu Ta Hana Jam’iyyun Siyasa 19 Kawo Tangarɗa Ga Zaɓen Ƙananan Hukumomi A Kano

Related

Yadda Aka Cafke Masu Saka Ƙwayoyi A Jakunkunan Matafiya A Filin Jirgin Sama A Kano
Manyan Labarai

Yadda Aka Cafke Masu Saka Ƙwayoyi A Jakunkunan Matafiya A Filin Jirgin Sama A Kano

6 hours ago
Gwamnatin Imo Ta Amince Da N104,000 A Matsayin Sabon Mafi Ƙarancin Albashin Ma’aikata 
Manyan Labarai

Gwamnatin Imo Ta Amince Da N104,000 A Matsayin Sabon Mafi Ƙarancin Albashin Ma’aikata 

13 hours ago
Jirgin Ƙasan Abuja-Kaduna Ya Yi Hatsari, Ba A San Halin Da Fasinjoji Ke Ciki Ba
Manyan Labarai

NRC Ta Dakatar Da Sufurin Jirgin Ƙasan Abuja-Kaduna Bayan Hatsarin Da Ya Yi 

17 hours ago
PDP Na Tattaunawa Da Obi Da Jonathan Kan Yi Mata Takarar Shugaban Ƙasa A 2027 – Moro
Manyan Labarai

PDP Na Tattaunawa Da Obi Da Jonathan Kan Yi Mata Takarar Shugaban Ƙasa A 2027 – Moro

19 hours ago
Kwalara Ta Kashe Mutum 7 A Zamfara, Sama Da Mutum 200 Sun Kamu Da Cutar
Manyan Labarai

Kwalara Ta Kashe Mutum 7 A Zamfara, Sama Da Mutum 200 Sun Kamu Da Cutar

20 hours ago
Jami’an Tsaro Sun Ceto Mutane 128 Daga Hannun ‘Yan Bindiga A Zamfara
Manyan Labarai

Jami’an Tsaro Sun Ceto Mutane 128 Daga Hannun ‘Yan Bindiga A Zamfara

1 day ago
Next Post
Kotu Ta Hana Jam’iyyun Siyasa 19 Kawo Tangarɗa Ga Zaɓen Ƙananan Hukumomi A Kano

Kotu Ta Hana Jam’iyyun Siyasa 19 Kawo Tangarɗa Ga Zaɓen Ƙananan Hukumomi A Kano

LABARAI MASU NASABA

Tallafin Walwalar Jama’a: Yadda Gwamnatocin Biranen Kasar Sin Ke Jifan Tsuntsu Biyu Da Dutse Daya

Tallafin Walwalar Jama’a: Yadda Gwamnatocin Biranen Kasar Sin Ke Jifan Tsuntsu Biyu Da Dutse Daya

August 27, 2025
Firaministan Kasar Sin Ya Yi Kira Da A Bunkasa Cinikayyar Ayyukan Hidimomi Masu Inganci

Firaministan Kasar Sin Ya Yi Kira Da A Bunkasa Cinikayyar Ayyukan Hidimomi Masu Inganci

August 27, 2025
Yadda Aka Cafke Masu Saka Ƙwayoyi A Jakunkunan Matafiya A Filin Jirgin Sama A Kano

Yadda Aka Cafke Masu Saka Ƙwayoyi A Jakunkunan Matafiya A Filin Jirgin Sama A Kano

August 27, 2025
Adadin Cinikayyar Sin Da Kasashen Kungiyar SCO Ya Kai Matsayin Koli A Tarihi

Adadin Cinikayyar Sin Da Kasashen Kungiyar SCO Ya Kai Matsayin Koli A Tarihi

August 27, 2025
Jimilar Darajar Hada-Hadar Shige Da Fice A Fannin Bayar Da Hidimomi Ta Kasar Sin Ta Kai Yuan Tiriliyan 3.9 A Rabin Farko Na Shekarar Bana

Jimilar Darajar Hada-Hadar Shige Da Fice A Fannin Bayar Da Hidimomi Ta Kasar Sin Ta Kai Yuan Tiriliyan 3.9 A Rabin Farko Na Shekarar Bana

August 27, 2025
Gwamnan Katsina Ya Dawo Gida Domin Ziyara Ga Al’ummar Da ‘Yan Bindiga Suka Kai Wa Hari A Malumfashi

Gwamnan Katsina Ya Dawo Gida Domin Ziyara Ga Al’ummar Da ‘Yan Bindiga Suka Kai Wa Hari A Malumfashi

August 27, 2025
Kasar Sin Ta Yi Watsi Da Kiran Shiga Tattaunar Kwance Damarar Nukiliya Tare Da Amurka Da Rasha

Kasar Sin Ta Yi Watsi Da Kiran Shiga Tattaunar Kwance Damarar Nukiliya Tare Da Amurka Da Rasha

August 27, 2025
Sin Ta Sanar Da Cimma Nasarar Dashen Huhun Alade A Jikin Bil’Adama

Sin Ta Sanar Da Cimma Nasarar Dashen Huhun Alade A Jikin Bil’Adama

August 27, 2025
Nijeriya Za Ta Ɗaukaka Da Fasahar Ƙere-ƙere Da Tattalin Abinci – Tinubu

Nijeriya Za Ta Ɗaukaka Da Fasahar Ƙere-ƙere Da Tattalin Abinci – Tinubu

August 27, 2025
Sin Da Kasashen Afirka Za Su Rubuta Sabon Babin Hakkin Dan Adam Bisa Ci Gabansu

Sin Da Kasashen Afirka Za Su Rubuta Sabon Babin Hakkin Dan Adam Bisa Ci Gabansu

August 27, 2025
Talla

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In

Add New Playlist

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.