Tsohon dan wasan bayan Real Madrid da Manchester United kuma dan kasar Faransa, Raphael Varane, ya yi ritaya daga buga kwallon kafa yanada shekara 31.
Varane ya koma kungiyar kwallon kafa ta Como dake kasar Italiya a kyauta a watan Yuli amma ya ji rauni a gwiwarsa a wasansa na farko da Sampdoria a watan jiya.
- Muna Fatan Sterling Ya Bai Wa Mara Ɗa Kunya A Arsenal – Arteta
- An Gudanar Da Taro Mai Taken “A Rubuce A Sama: Labarina Na Kasar Sin” Don Murnar Cika Shekaru 75 Da Kafuwar Jamhuriyar Jama’ar Kasar Sin a Mexico da Australiya
Duk da haka, dan wasan bayan ya ce zai ci gaba da zama a kungiyar domin ya taimaka wa kungiyar a wasu hanyoyin da ba na shiga filin wasa ba.
Varane ya fara taka leda a kungiyar Lens ta Faransa inda ya shafe kakar wasa daya a kungiyar kafin ya koma Real Madrid a shekarar 2011.
Ya taka rawar gani na tsawon shekaru 10 a babban birnin Madrid na kasar Spain, inda ya lashe kofuna 18 – ciki har da kofunan La Liga uku da na gasar zakarun Turai hudu.
Mai tsaron bayan ya koma Old Trafford a lokacin bazara na shekarar 2021 kan fam miliyan 34, inda ya buga wasanni 95 a duk gasannin da ya bugawa Manchester United.
Ya lashe kofin Carabao a shekarar 2022 kuma wasansa na karshe a kungiyar shi ne nasarar cin kofin FA na karshe akan abokan hamayyar Man Utd wato Manchester City a Wembley a watan Mayu.
A bangaren wasannin kasa da kasa Varane ya buga wasansa na farko ga kasar Faransa a shekara ta 2013 inda ya buga mata wasanni 93 jimilla,sannan ya lashe gasar cin kofin duniya a shekarar 2018, da gasar Nations League a shekarar 2021 kuma ya sake kai wasan karshe na gasar cin kofin duniya a shekarar 2022.
“Ba ni da nadama, ba zan canza komai ba, na yi nasara fiye da burin da nake dashi,ina kuma alfahari da cewa na yi kokarin barin ko’ina fiye da yadda na same shi inji Varane a wani rubutu da yayi a shafinsa na sada zumunta.