Shugaban Kamfanin Rukunonin Dangote, Aliko Dangote, ya bayyana cewa, kamfanin tace man fetur na kasa NNPCL, ya tabka babban kuskure a kan rage hannun jarinsa zuwa kaso 7. 2, a cikin dari, a cikin yarjejeniyar man Dangote da kamfanin na NNPCL.
Aliko, ya sanar da hakan ne, a wata tattaunawa a kwanan baya da Bloomberg.
Ya ce, a ka’ida kamata ya yi, kamfanin NNPCL kaso 20 a cikin dari a matatar man ta Dangote, amma a yanzu, ya rage zuwa kaso 7.2 a cikin dari.
- Yawan Cinikayyar Waje Ta Sin A Fannin Hajoji Da Bayar Da Hidimomi Ya Karu Da Kaso 4% A Agusta
- Rodri Ba Zai Sake Buga Kwallo A Wannan Kakar Ba Sakamakon Rauni
Aliko ya ci gaba da cewa, tun da farko kamfanin na NNPCL ya amince da yarjejeniyar ce, a kan dala biliyan 2.79, wadda ta had har da far biyan dala biliyan 1.
Ya kara da cewa, sai dai, bayan an kaulla wannan yarjejeniyar, sai kamafnin na NNPCL, ra rage shiyarsa, inda ragewar da NNPCL ya yi babban kuskure ne.
Bisa wannan bayanin da Aliko ya yi, hakan ya nuna a zahairi cewar, yajejeniyar a tsakanin kamfannin biyu, ta kullu.
A cewarsa, a jarjeniyar ta farko kamfanin na NNPCL zai biya mu dala biliyan 1 ne, wadda take daya daga cikin yarjeniyar da aka kulla, da ta kai ta akalla, dala biliyan 2.79.
Ya kara da cewa, NNPCL ya biya dala biliyan 1 a cikin shekara daya da rabi, wanda sauran biyan kudin, aka kasa su zuwa gida biyu.
Aliko ya ci gaba da cewa, a kaso na farko a duk lokacin da NNPCL ya kawo mana kimanin Ganguna danyen mai 300,000, wanda mu yi ragin dala biliyan 2 daga cikin sauran kudin, har sai an biya sauran bashin gaba daya, amma NNPCL yaki aminta da hakan, wanda hakan ya jefa su, a cikin rudani ko kuma dai, akwai rashin fahimta.
Ya ci gaba da cewa, NNPCL, sun nuna cewa, sam-sam ba sa son wannan yarjejeniyar ta cire kudin, wanda suka gwammace, su biya sauran kudin da suka rage.
Aliko ya kara da cewa, daga baya NNPCL, ya sake sanya hannu a wata sabuwar yajejeniya domin ya sauya jarjejeniyar da ka yi ta farko.
A cewarsa, a wannan sabuwar yarjejeniyar NNPCL ya amince ya biya mu sauran dala biliyan 1.8, amma ba tare da biyan kudin ruwa ba, bayan shekara daya.
Ya ce, a ka’ida watan Yuni ne aka sanya amma suka sake dawo wajen mu suka sheda mana cewa, sun sauya shawararsu.
Aliko ya kara da cewa, sun dage a kan kashi 7.2 a cikin dari mai makon kashi 20 a cikin dari da aka kaulla yarjejeniyar ta farko, wanda a yanzu, muka aminta da bukatar ta su.
A cewarsa, suna da kashi 7.2 a cikin dari, mu kuma mun kasance, muna da sauran kudin.