Gwamantin kasar Afrika ta Kudu zata rage farashin litar man fetur daga ranar Laraba, mai zuwa.
Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da kasar ke fuskantar matsin rayuwa da hauhawar farashin kayayyakin masarufi.
Sanarwar hakan ta fito ne ta bakin Ministan Makamashi da Albarktun kasar, Gwede Mantashe, a ranar Asabar.
Ya ce manufar ragin shi ne saukakawa masu amfani da makamashin samunsa cikin sauki.
Mantasha ya ce gwamnati ta dauki matakin ne duba da yadda ake samun karancin masu sayen man fetur a kasar sakamakon matsin tattalin arziki da kasar ta tsinci kanta a ciki tun bayan bankewar cutar Korona.
Haka zalika, Ministan ya kara da cewa ”Matakin da kasashe masu arzikin man fetur (OPEC) da wanda basu da shi suka dauka na kara yawan adadin samar da man ya ba da gagarumar gudunmawa ga masana’antu”.
Idan za a iya tunawa a watan Yuni, 2022 ne kasar Afirka ta Kudu ta fuskanta na matsanancin hauhawar farashi kayayyaki da ba ta taba gani ba wanda ya kai adadin 7.4 a shekaru 13 da suka gabata.
Kasashe da dama a duniya na fuskantar matsin tattalin arziki, inda a kasashen Afrika ake samun hauhawar farashi na kayan masarufi, inda wasu kasashen aka fara matsa wa gwamnatoci lamba.