Zaunannen wakilin kasar Sin a Majalisar Dinkin Duniya Fu Cong ya bayyana cewa, kasar Sin ta damu matuka game da halin da ake ciki tsakanin kasashen Lebanon da Isra’ila, kana tana nuna adawa da duk wani harin wuce gona da iri kan fararen hula dake keta dokokin jin kai na kasa da kasa.
Fu ya bayanna hakan ne a jawabin da ya gabatar a taron kwamitin sulhu na MDD kan halin da ake ciki a Labanon da Isra’ila a Laraba, inda ya ce al’ummar Lebanon sun fuskanci mako mafi tashin hankali cikin shekaru da dama, inda dubban na’urorin sadarwa suka tarwatse a lokaci guda wanda ya janyo hasarar rayukan fararen hula da ba su ji ba su gani ba, kana mutane 500 sun mutu yayin da wasu kusan 2,000 suka jikkata a wasu manyan hare-hare ta sama da Isra’ila ta kaddamar.
Kasar Sin tana matukar goyon bayan kasar Lebanon wajen kare ’yancinta, da tsaro, da martabar kasa, kuma tana yin Allah wadai da ayyukan da suka saba wa ka’idojin dangantakar kasa da kasa, inda ya kara da cewa, bai kamata yankin Gabas ta Tsakiya ya sake afkawa cikin wani yaki ba, don haka ya zama wajibi a dakatar da aikin soja da tsagaita bude wuta. (Mai Fassara: Mohammed Yahaya)