An yi wata arangama tsakanin mayakan kungiyar Taliban da ke mulkin Afganistan da wasu dakarun da ke gadin iyakar kasar Iran a kan iyakar kasashen biyu, inda mutum guda daga cikin mayakan na Taliban ya rasu sakamakon artabun.
An yi arangamar a ranar Lahadi a kan iyakar da ke tsakanin lardin Nimroz na Afghanistan da Hirmand na Iran.
- Da Dumi-Dumi: ASUU Ta Tsawaita Yajin Aikinta Zuwa Makonni 4
- Daukacin Gwamnoni Za Mu Hada Kai Don Share Wa NLC Hawaye – Gwamna Ganduje
Sai dai kuma bayan faruwar lamarin kasashen biyu sun shiga cacar-baki da zargin juna da alhakin janyo fadan da ya ci rai guda.
Kazalika wannan shi ne fada na farko da ya barke tsakanin kasashen biyu tun bayan da kungiyar Taliban ta kwace iko a Afghanistan shekara daya da ta wuce.
A watan da ya gabata, Iran ta ba da rahoton mutuwar daya daga cikin masu gadinta a wani lamari da ya faru a wannan yanki.
Ba a san hakikanin yanayin fadan na baya-bayan nan ba, amma wani rahoton Iran ya ce an fara harbe-harbe ne a lokacin da kungiyar Taliban suka yi kokarin daga tutarsu a yankunan da ba na Afghanistan ba.