Kwamitin Majalisar Dattijai na gyaran kundin tsarin mulkin 1999 ya fara wani taron tattaunawar kwanaki biyu a Kano, tare da nufin kammala aikin gyaran kundin tsarin mulki kafin watan Disamba 2025.
Taron, wanda aka shirya tare da haɗin gwuiwar Cibiyar Tsarin Dokoki da Inganta Siyasa (PLAC), na da nufin magance batutuwan da suka haɗa da ƴancin ƙananan hukumomi, da kafa ƴansandan jihohi, da kuma bai wa Sarakunan gargajiya dama a gwamnatance domin magance matsalar tsaro.
- Sanata Barau Jibrin Ya Ƙaddamar Da Motocin Zirga-Zirga A Kano
- Jihar Kano Ta Musanta Zargin Karɓar Bashin Biliyan 177 Daga Faransa
Masu jawabi, ciki har da Sanata Jibrin Barau, Mataimakin Shugaban Majalisar Dattijai, sun jaddada mahimmancin haɗin kai da masu ruwa da tsaki kamar gwamnoni, da majalisun jihohi, da ɓangaren shari’a, da ƙungiyoyin farar hula domin tabbatar da samun nasarar wannan gyara.
Barau ya yi kira da a samar da hadin kai tsakanin dukkan ɓangarorin majalisar dokoki guda biyu sannan ya buƙaci a yi la’akari sosai da shawarwarin da za su kawo canji mai ɗorewa ga al’ummar Nijeriya.
Mataimakin Shugaban Majalisar Wakilai, Benjamin Kalu, ya jaddada mahimmancin ɗaukar mataki cikin lokaci da kuma tsara ayyuka yadda ya dace domin kaucewa karkatar da hankalin jama’a yayin da zaɓe ke gabatowa.
Kwamitocin majalisar dattijai da na wakilai sun shirya gudanar da tarukan sauraron ra’ayoyin jama’a tare da Sarakunan gargajiya da shugabannin siyasa domin samun cikakken bayani.
Sauran masu jawabi, ciki har da Hon. Adebo Edward Ogundoyin, Shugaban Taron Shugabannin Majalisun Jihohi, da tsohon Shugaban Majalisar Dattawa Ahmad Lawan, sun buƙaci a mayar da hankali kan ƴancin mata, da ƴancin ƙananan hukumomi, da kuma rawar da Sarakuna zasu iya takawa a hukumance.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp