Hukumar Hana cin hanci da rashawa (ICPC) ta rattaba hannu kan wata muhimmiyar yarjejeniyar haɗin gwuiwa da hukumar binciken nuhalli ta birnin London (EIA) domin magance cin hanci daga jami’an gwamnati, musamman kan laifuka masu alaƙa da muhalli.
An sanya hannu kan yarjejeniyar a ranar 20 ga Satumba, 2024, tare da Shugaban ICPC, Dr. Musa Aliyu, SAN, da Jagoran Shirin Tabbatar da Adalci na EIA, Justin Gosling. Wannan haɗin gwuiwar zai ba da damar ƙarin haɗaka da musayar bayanai tsakanin ƙungiyoyin biyu.
- ICPC Da NITDA Sun Kulla Alakar Aiki Don Yaki Da Rashawa Ta Hanyar Fasaha
- Kasar Sin Ta Nuna Damuwa Kan Rikicin Isra’ila Da Lebanon
Dr. Aliyu ya nuna muhimmancin magance cin hanci da ya shafi laifukan muhalli kamar safarar namun daji, gurbacewar muhalli, da ayyukan da ke taimakawa canjin yanayi, wanda ya bayyana a matsayin barazana ga ‘yan Nijeriya. Ya nuna fatan wannan haɗin gwuiwar zai ƙara inganta martabar ICPC wajen yaƙi da irin waɗannan laifukan.
Hukumar EIA, wadda ta fara aiki a Nijeriya da yankunan Afrika ta Yamma da ta tsakiya kusan shekaru biyar da suka gabata, ta mayar da hankali kan haɓaka ƙwarewa wajen bincike, da haɗin kai da masu shigar da ƙara da fannin shari’a, tare da goyon bayan ƙungiyoyin farar hula wajen yaƙi da laifukan muhalli.