Gwamnan Jihar Adamawa, Ahmadu Fintiri, ya yi afuwa ga fursunoni biyu domin murnar Ranar ‘ƴancin Nijeriya.
Fursunonin, Chai Yerima da Mohammed Bapeto, sun samu ‘yanci daga tsohuwar cibiyar tsare fursunoni ta Yola da kuma cibiyar tsare fursunoni ta Jada.
- Fintiri Ya Nada Farfesa Gidado Da Wasu 4 Hukumar Gudanarwar Jami’ar Adamawa
- Mutane 4 Sun Rasu Sanadin Kwalara A Adamawa
Afuwar ta biyo bayan shawarwarin kwamitin da aka kafa tare da bin sashi na 212 (i) (d) na kundin tsarin mulkin Nijeriya.
Gwamna Fintiri ya umarci a sake su nan take tare da jan hankalinsu da su yi amfani da wannan dama don gyara halayensu da kuma komawa cikin al’umma a matsayin masu bin doka.
Ya kuma shawarce su da su mayar da hankali kan kimtsa kansu, neman ilimi, da koyon sana’o’i, su sake haɗe kai da iyalansu da al’ummarsu, tare da yin amfani da wannan sabuwar damar da suka samu.