Gwamna Ahmadu Umaru Fintiri na Jihar Adamawa, ya amince da sake fasalin majalisar gudanarwar Jami’ar Jihar da ke Mubi, inda ya nada Farfesa Maxwell Gidado (SAN) a matsayin shugaban hukumar gudanarwar Jami’ar.
Sauran mambobin hukumar gudanarwar sun hada da Alhaji Aliyu Mohammed Gabdo, Mista Vidon Jaule, Dakta Ali Danburam da Barista Hapsat Abdullahi Jimeta.
- Babban Yankin Kasar Sin Na Maida Hankali Sosai Kan Bala’ in Girgizar Kasar Da Ya Afkawa Taiwan
- Gwamnatin Kano Ta Haramta Shirya Fina-finan Daba Da Harkar Daudu A Jihar
Sanarwar ta ce sake kafa hukumar gudanarwar ya ta’allaka ne da ikon da dokokin da suka kafa Jami’ar suka bai wa gwamnan jihar.
Nadin Farfesa Gidado da sauran mambobin yana kara tabbatar da kudurin gwamnatin jihar na ganin an samu nagartaccen ilimi da tsarin gudanarwa a jami’ar.
Mista Humwashi Wonosikou, babban sakataren yada labaran gwamnan, a wata sanarwar da ya fitar, ya ce za a gudanar da bikin kaddamar da hukumar gudanarwar a hukumance a ranar Juma’a 5 ga Afrilu, 2024 a dakin taro na gidan gwamnati.