Sanata mai wakiltar Borno ta Kudu a majalisar dattawa, Mohammed Ali Ndume, ya yi kira ga shugaban kasa Bola Tinubu da ya dauko sojojin haya don kawar ‘yan ta’addan Boko Haram a Jihar Borno.
Ndume, ya yaba da irin rawar da sojojin Nijeriya ke takawa, amma ya ce ba su da kayan aikin da za su yaki ‘yan tada kayar baya a yankin Arewa maso Gabas.
- Saudiyya Ta Taya Nijeriya Murnar Cika Shekaru 64 Da Samun ‘Yancin Kai
- Jirgin Ruwa Dauke Da ‘Yan Maulidi 200 Ya Nutse A Neja
Ya ce manyan kasashen duniya suna daukar sojojin haya don taimaka musu a yaki da ‘yan ta’adda.
Ya ce kasashe irin su Amurka da Rasha da Birtaniya da Faransa da dai sauransu, suna amfani da sojojin haya.
Sanatan ya bayyana cewa matakin zai kasance na wucin gadi.
Ndume, ya yi wannan kiran ne a kan yadda ‘yan ta’addan Boko Haram suka kashe wasu manoma shida a garin Ngoshe da ke karamar hukumar Gwoza ta Jihar Borno, tare da sace wasu biyar da suka hada da mata.
Ya koka da yadda hare-haren Boko Haram ke tilastawa manoma barin amfanin gonakinsu daidai lokacin da kasar ke fama da matsalar karancin abinci.
“A duk fadin duniya, gwamnatoci suna daukar hayar sojoji don shiga wasu wurare. Shugaba Bola Ahmed Tinubu na iya daukar wannan mataki na wucin gadi. Wadannan sojoji za su iya aiki da Civilian JTF kafada da kafada.
“Wadannan ‘yan kwangila za su zo da kayan aikinsu da kayan aikin soja. A cikin kankanin lokaci, za su kawar da ‘yan ta’addar Boko Haram.
“Ana kuma iya amfani da su wajen kawar da ‘yan fashin daji a Arewa maso Yamma.
“Gwamnatin Tarayya za ta iya daukar matasa aikin soja akalla miliyan daya. Hakan zai taimaka wajen yaki da ta’addanci.”
LEADERSHIP ta ruwaito cewa a baya-bayan nan, ‘yan ta’addan sun kashe kwamandan Civilian JTF, Jubril Dada Zarana.
Sabon harin na zuwa ne ‘yan makonni kadan bayan da ‘yan ta’addan suka kashe mutane da dama a ta hanyar amfani da bam.