Sanata mai wakiltar Kudancin Borno, Ali Ndume, ya ce dagangan aka rikirkita tsarin zaben Nijeriya domin a samu damar yin magudi.
Ndume ya bayyana hakan ne a wata tattaunawa da manema labarai a Kano bayan ya halarci taron majalisar dattawa kan sake duba kundin tsarin mulkin kasar nan.
- Ndume Ya Bukaci Tinubu Ya Dauko Sojojin Haya Don Yakar ‘Yan Ta’adda
- Ranar ‘Yanci: Jihar Kano Ta Zama Madubin Dubawa A Kan Kyakkyawan Shugabanci – Gwamna Abba
Tsohon shugaban masu rinjaye na majalisar dattawa, ya nuna shakku kan bukatar samar da sabuwar hukumar da za ta gudanar da zabuka a duk bayan shekaru hudu, yana mai cewa hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) da ake amfani da ita za ta iya daukar wadannan ayyuka.
Ya kuma nuna rashin jin dadinsa da sarkakiyar tsarin zaben Nijeriya, wanda ya yi imanin cewa an tsara shi ne domin karfafa magudi.
“Ina goyon bayan cin gashin kan kananan hukumomi da ra’ayin INEC ta gudanar da zaben kananan hukumomi. Wani batu da ake tattaunawa a majalisar dokokin kasar nan shi ne, batun kafa wata sabuwafr hukumar zabe ta kananan hukumomi, kuma ni ba na goyon bayan hakan.
“Dagangan aka rikita zabuka a Nijeriya don ba da damar yin magudi. Me ya sa ba za mu kafa dokokin da ke tabbatar da kirga kuri’un ba? Me zai hana ‘yan kasa su yi zabe a wayoyinsu? Me ya sa ba za a bari INEC ta sanya ido a zabuka ta hanyar fasaha da kuma samar da dakin bincike ba? Manhajar Google na iya gaya muku wurin da kuke a lokacin da ake bukata, don haka me ya sa ba za mu iya amfani da fasaha wajen gudanar da zabukanmu ba?” Ya tambaya.
Dan majalisar ya ci gaba da cewa, matsalar da ke tattare da tsarin zaben Nijeriya shi ne, rashin gaskiya, rashin jin tsoron Allah a tsakanin shugabannin siyasa.