Jam’iyyar APC tashe dukkan kujerun shugabancin ƙananan hukumomi 27 da kujerun kansila 281 daga cikin kujeru 287 da aka yi takara a zaɓen ƙananan hukumomi na ranar 5 ga watan Oktoba, 2024 a Jihar Jigawa.
Jam’iyyar APGA ta samu kujerar kansila ɗaya a karamar hukumar Guri, yayin da jam’iyyar Accord ta samu kujeru huɗu a ƙananan hukumomi Taura, Jahun, Gagarawa, da Gwuiwa. Jam’iyyu 11 ne suka shiga wannan zaɓe.
Hukumar Zaɓe ta Jihar Jigawa (JISEC) ta bayyana sakamakon zaɓen a shalƙwatar ƙananan hukumomi da wuraren haɗa sakamakon zaɓe a yankunan siyasa. Amma, ba a bayyana sakamakon zaɓen kansila na yankin Dubantu a ƙaramar hukumar Hadejia ba saboda matsalar da aka samu wajen ƙirga ƙuri’u da lalata akwatin zaɓe. Shugaban JISEC, Auwalu Muhammad Harbo, ya miƙa takardun shaidar nasara ga shugabannin ƙananan hukumomin da suka yi nasara.
Shugaban jam’iyyar APC na jihar, Aminu Sani Gumel, ya yaba wa mambobin jam’iyyar bisa wannan gagarumar nasara, yana danganta ta da amincewar jama’a da jagorancin Gwamna Namadi da tsare-tsarensa 12 na ci gaban Jihar Jigawa. Ya kuma jaddada cewa ‘yan Jihar Jigawa sun ƙi jam’iyyun da ba su da ingantattun tsare-tsaren cigaba.