Jakadan kasar Bulgariya a Nijeriya Mista Yanko Yordanob, ya ayyana kudurin kasarsa, wajen yin hadaka da jihar Filato a fannin aikin noma da samar da tsaro, da illimin zamani da kuma yawon bude ido.
A cewarsa, yin hadaka musamman za ta kara habaka tattalin arzikin jihar da kuma kara karfafa dankon huddar jakandanci a tsakanin Nijeriya da kasar ta Bulgariya.
Jakada Yordanob, ya sanar da hakan ne, a yayin da ya kai ziyarar aiki ga gwamnana jihar Caleb Mutfwang a fadar tsohowar gidan gwamnatin jihar ta, Rayfield da ke a birnin Jos.
Ya sanar da cewa, jihar Filato na da albarkatun noma da gurane yawon bude ido, saboda dausayin da ake da shi jihar, ta kasance ta na da kyakyawan yanyi na zaman lafiya da nuna kara ga bakin da suka shogo cikin jihar.
Yordanob ya ci kara da cewa, “Mun zabi manyan bangarori uku na yin huddar jakandanci a tsakanin Nijeriya da kasar mu ta Bulgariya, musamman a fannin aikin noma na jihar Filato da samar da tsaro da ilimin zaani
Ya sanar da cewa, kasar ta Bulgariya, za ta taimakwa jihar Filato a fannin yin aikin noma na zamani, musamman domin a bunkasa noam don samun riba.
A na sa jawabin gwamnan jihar Caleb Mutfwang, ya nuna jin dadinsa a kan ziyarar aikin da jakadan ya kawo zuwa jihar da kuma shirin na yin hadaka a tsakanin jihar da kasar ta Bulgariya,
Ya sanar da cea, tuni gawmnatin jihra ta alkanta kanta da aikin noma na gwamnatin tarayya, musamman domin jihar ta cimma burinta na kara samar da wadataccen abinci a jihar.