Assalamu alaikum masu karatu, barkan mu da sake haduwa da ku a wannan makon a cikin shirinmu mai farin jini da albarka na Ado Da Kwalliya.
Inda za mu yi magana akan abubuwan da za su biyo baya bayan mace ta haihu ta haihu da sati biyu.
- Wata Mata Ta Sace Jariri Sabuwar Haihuwa A Asibiti A Nasarawa
- Tsarin Tazarar Haihuwa Mara Amfani Da Magani (2)
Idan kin haihu, rainon jariri da tarbiyyar ‘ya’ya:
Sai ki fara shirya jikinki don tarbar maigida, don in dai lafiya kika haihu daga lokacin za ki tsinci kanki cikin kuzari. Duk wanda ya ganki zai ganki tas kamar ba ki haihu ba. Don haka tun da lafiyar ta samu sai a fara shirya jiki, ki yi kokarin a dafa miki kaza irin ta masu jego ki fara ci, idan babu kada ki matsa wa mijinki. Cin kazar yana kara gyaran kasan mace maigida ya ji ta zan-zan kamar ba ta haihu ba.
Shan ‘ya’yan itatuwa akai-akai barin ma kankana, abarba, gwanda, lemon zaki.
Ki dinga yin kunun aya kina sha, in zai samu ki yi kullum, amma sukari dan kadan za ki dinga sawa ko ki sha haka.
Shan maganin mata mai kyau (habbatus-sauda, zuma, dabino, aya, madara, nono amma mai kyau, shan zuma madi, tsimi da sauransu.
Tun daga ranar da kika haihu har zuwa lokacin da za ki yi arba’in ki zama cikin tsaftace jiki da gyaran jiki, gyaran jariri, gyaran gida.
Kuma kar ki yi sake da yin turaren wuta da na jiki a gidanki da jikinki, don wasu matan idan suka haihu, sai ka ganta ragajab ba tsaftace jiki ko ina su a ganin su idan ana jego ba a gyaran jiki tun da mijinta ba ya tare da su a shimfida, kana zuwa kusa da su sai ka ji wari da karni, wanda a Musulunci ko yau mace ta haihu jini ya dauke mata a ranar da ta haihu, mijinta yana da ikon zuwa ya sadu da ita a rana