Assalamu alaikum masu karatu, barkanmu da sake haduwa da ku a wannan makon a cikin shirin namu mai farin jini fa albarka na Girki Adon Mata.
A yau Shafin namu zai koya muku yadda ake madarar waken soya wato (Soya Beans Milk).
Abubuwan da Uwargida za ta tanada:
Waken soya, kanwa, madara fauda, filaibo, beby mid, sodium, ruwa:
Da farko za ku jika waken soyar ya jiku sosai saboda gafinsa ya fita sannan ya yi haske sosai, sai ki wanke shi ki cire tsakuwar dake ciki wato ki rege shi, sai ki samu kanwa ungurno ki sanya a ciki ‘yar daidai gwargwadon yadda za ki yi.
Misali idan na mudu daya ne sai ki sa kanwar goma ta ishe ki, sai ki kai nika ani ka tare da kanwar sai ki dora ruwa a wuta in ya tafasa, sai ki juye kullin a cikin ruwan zafin, sai ki jujjuya shi ya hade jikinsa, ki rufe shi amma fa ki zauna a wurin saboda bori da yake yi don kar ya zube.
Idan ya tafasa sau biyu ko uku, sai ki sauke shi ki jujjuya shi ya sha iska kadan, sannan ki samu abin tata ki tace shi ki kai shi waje mai dan dumi ki rufe shi ya samu kamar awa bakwai zuwa takwas za ki ga ya yi kauri so, kuma kar ki cika masa ruwa a wurin tatar.
Sai ki sami mabirgi ki birge shi sosai ya yi sumut za ki ganshi ya yi kamar kindirmo, sannan ki zuba milk powder filaibo, baby mid, sodium amma kadan za ki sa sodium din ki sa duk kayan hadin da na ambata miki sai kii juya su, sannan idan kina so za ki iya sa kwakwa sai ki gurza ta ki zuba tana kara masa dadi.
Wani hadin:
Idan kika kai nika aka nika miki, sai ki fara tace shi kafin ki dora a wuta amma kar ki sa masa ruwa da yawa, bayan kin tace sai ki dora shi a wuta shima ki zauna a wajen saboda kar ya yi bori ya zuba, idan ya tafasa sai ki bude shi ki barshi ya yi ta tafasa har sai ya dahu, idan ya dahu yana cire gafin waken, sai ki sauke shi ki bar shi ya sha iska daga nan ki kawo wadancan kayan hadin da muku ambata na farko ki zuba.
Shima idan kina so za ki iya sa masa gurzazziyar kwakwar tana kara masa dadi.
Asha dadi lafiya