Shugaban kasar Kamaru, Paul Biya ya koma Yaoundé, babban birnin kasar, bayan watanni bakwai da barin kasar, inda aka dinga rade-radin ya mutu.
Da misalin karfe 5:30 na yammancin ranar Litinin ne jirgin shugaban da iyalinsa ya sauka a babban filin jirgin saman Nsimalen.
- Fursunoni 11 Sun Kammala Digiri A Gidan Yari na Kaduna
- Ciwon Daji: Adadin Masu Warkewa A Nijeriya Ya Yi Kaɗan – Pink Africa
Magatakardan fadarsa, Ferdinand Ngoh da sauran jami’an gwamnati da manyan ‘yan majalisa ne suka tare shi.
Magoya bayan Paul Biya, karkashin jam’iyya mai mulki RDPC sun tarbe shi a fadin titunan birnin, domin nuna murnar dawowarsa.
Paul Biya mai shekara 92 a duniya, ya kasance a kan karagar mulki tun kimanin shekara 42.
Ana sa ran zai sake tsayawa takarar shugaban kasa a zaben shekara mai zuwa.