• English
  • Business News
Sunday, October 26, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Matsalar Tsaro: Gwamnonin Zamfara Da Katsina Sun Gana Da Ministan Tsaro Da Ribaɗu

by Leadership Hausa and Sulaiman
1 year ago
Zamfara

Gwamnan jihar Zamfara Dauda Lawal da takwaransa na jihar Katsina Dikko Umar Raɗɗa sun yi wata ganawar sirri da Ministan tsar, Badaru Abubakar da mai bai wa shugaba ƙasa shawara kan harkokin tsaro, Nuhu Ribaɗu.

Waɗannan ganawa guda biyu sun gudana ne a jiya Talata a ma’aikatar tsaro ta tarayya da kuma ofishin mai bai wa shugaban ƙasan shawara kan harkokin tsaro.

  • Za Mu Fara Kamen Mabarata A Abuja – Wike
  • An Watsa Shirin Bidiyo Zagaye Na 3 Mai Taken “Bayanan Magabata Da Xi Jinping Yake So” A Rasha

A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan jihar Zamfara, Sulaiman Bala Idris ya fitar yau, ya bayyana cewa, taron ya yi zuzzurfan tattaunawa game da shawarwarin da haɗaɗɗiyar ƙungiyar ƙungiyoyin Arewa ta ‘Coalition of Northern Groups (CNG)’ ta bayar.

LABARAI MASU NASABA

Nafisa Abdullahi Aminu: Yarinyar Da Ta Ɗaukaka Darajar Nijeriya A Idon Duniya

Gwarzon Banki Na Shekarar 2025 Bankin Providus

Sanarwar ta yi ƙarin haske da cewa, haɗaɗɗiyar ƙungiyar ‘yan Arewar ta gudanar da wani taro ne na kwana biyu a Abuja a ranar 23 ga watan Janairun 2024, wanda tsohon shugaban ƙasa, Janar Abdussalami Abubakar ya shugabanta.

Sanarwar ta Idris ta ce, “jiya Gwamna Dauda Lawal na jihar Zamfara da Gwamna Dikko Umar Raɗɗa na jihar Katsina sun gana da Ministan tsaro Badaru Abubakar a ma’aikatar tsaro da ke Abuja.

“Gwamnonin sun tattauna muhimman batutuwan da suka shafi tsaro a jihohin biyu, tare da samar da hanyoyin bi, bisa haɗin gwiwa da ma’aikatar tsaron don magance matsalar.

“Bayan zaman da ya gudana ma’aikatar rsaron, sai Gwamnonin biyu tare da Ministan tsaron, suka wuce zuwa ofishin mai ba shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro don gudanar da wani zaman na musamman.

“A wannan zaman tattaunawar ne suka amince da shawarwarin da aka bayar da wancan taro, wanda haɗaɗɗiyar ƙungiyar ‘yan Arewar ta bayar.

“A cikin watan Janairun shekarar nan ne haɗaɗɗiyar ƙungiyar ƙungiyoyin Arewa ta gabatar da wani taron tattaunawa, wanda tsohon shugaban ƙasa, Janar Abdussalami Abubakar, tare da halartar wasu fitattun masu ruwa da tsaki daga yankin Arewacin ƙasar nan.

“Aiwatar da waɗannan shawawarin da wannan kwamiti na tsaro ya bayar, zai taimaka matuƙa wajen magance wannan tsalar tsaro mai rikitarwa da ta addabi Arewa Nijeriya.

“Wannan na cikin dabarbaru da haɗin gwiwar da waɗannan gwamnoni na Zamfara da Katsina suke bi don ganin sun kawo ƙarshen ‘yan bindiga a jihohin su.

Wakilan wannan Ƙungiya ta ‘Coalition of Northern Groups (CNG)’ na cikin wannan tattaunawa da aka yi, bisa wakilcin shugaban kwamitin amintattu na Ƙungiyar, Nastura Ashiru Shariff; shugaban kwamitin tsaro na ƙungiyar, Alhaji Bashir Yusuf; Alhaji Ibrahim Ahmed Katsina; Janar Sarkin Yaki Bello, Ambasada Buhari Bala da Janar Sa’ad Abubakar.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Labarai

Nafisa Abdullahi Aminu: Yarinyar Da Ta Ɗaukaka Darajar Nijeriya A Idon Duniya

October 25, 2025
Gwarzon Gwamnan 2025, Biodun Abayomi Oyebanji
Manyan Labarai

Gwarzon Banki Na Shekarar 2025 Bankin Providus

October 25, 2025
Gwarzuwar Hukumar Da Ta Kawo Sauyi A Kula Da Muhalli A 2025 Hukumar NASENI
Manyan Labarai

Gwarzuwar Hukumar Da Ta Kawo Sauyi A Kula Da Muhalli A 2025 Hukumar NASENI

October 25, 2025
Next Post
Sarki Sanusi II Zai Naɗa Babban Ɗansa A Matsayin Ciroman Kano

Sarki Sanusi II Zai Naɗa Babban Ɗansa A Matsayin Ciroman Kano

LABARAI MASU NASABA

An Yi Liyafar Murnar Kebe Ranar Tunawa Da Kawo Karshen Mulkin Mallakar Japan A Yankin Taiwan

An Yi Liyafar Murnar Kebe Ranar Tunawa Da Kawo Karshen Mulkin Mallakar Japan A Yankin Taiwan

October 25, 2025

Nafisa Abdullahi Aminu: Yarinyar Da Ta Ɗaukaka Darajar Nijeriya A Idon Duniya

October 25, 2025
Sin Da Amurka Sun Fara Tattaunawa Kan Tattalin arziki Da Cinikayya A Kuala Lumpur

Sin Da Amurka Sun Fara Tattaunawa Kan Tattalin arziki Da Cinikayya A Kuala Lumpur

October 25, 2025
Gwarzon Gwamnan 2025, Biodun Abayomi Oyebanji

Gwarzon Banki Na Shekarar 2025 Bankin Providus

October 25, 2025
Firaministan Sin Ya Isa Singapore Don Ziyarar Aiki

Firaministan Sin Ya Isa Singapore Don Ziyarar Aiki

October 25, 2025
Gwarzuwar Hukumar Da Ta Kawo Sauyi A Kula Da Muhalli A 2025 Hukumar NASENI

Gwarzuwar Hukumar Da Ta Kawo Sauyi A Kula Da Muhalli A 2025 Hukumar NASENI

October 25, 2025
An Gudanar Da Taron Cika Shekaru 80 Da Kawo Karshen Mulkin Mallakar Japan A Yankin Taiwan Da Dawo Da Shi Kasar Sin A Beijing

An Gudanar Da Taron Cika Shekaru 80 Da Kawo Karshen Mulkin Mallakar Japan A Yankin Taiwan Da Dawo Da Shi Kasar Sin A Beijing

October 25, 2025

Daɓid Adeyemi

October 25, 2025
Wakilin Sin: Shawarar GGI Ta Nuna Yadda Za A Jagoranci Bunkasa Makomar MDD

Wakilin Sin: Shawarar GGI Ta Nuna Yadda Za A Jagoranci Bunkasa Makomar MDD

October 25, 2025
Gwarzuwar Ma’aikaciyar Jinya Ta Shekarar 2025: Misis Mabel Ijeoma Duaka

Gwarzuwar Ma’aikaciyar Jinya Ta Shekarar 2025: Misis Mabel Ijeoma Duaka

October 25, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.