A yau Alhamis, shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya halarci taron tattaunawa na jagororin kungiyar “BRICS+”, wanda ya gudana a cibiyar nune nune ta birnin Kazan na kasar Rasha, inda kuma ya gabatar da muhimmin jawabi.
Cikin jawabin na sa mai taken “Tattaro karfin gaske na kasashe masu samun saurin ci gaba, da masu tasowa, don ingiza gina al’umma mai makomar bai daya ga daukacin bil adama”, shugaban na Sin ya ce hadin gwiwar wadannan muhimman sassa a lamace ta zahiri dake nuna faruwar babban sauyi a duniya.
- ‘Yan Bindiga Sun Kashe ‘Yansanda 4 A Katsina
- Sojoji Sun Ceto Mata 3, Sun Kwato Makamai A Katsina Da Zamfara
Ya ce kamata ya yi kasashe mambobin BRICS, su nuna basira, da karfin su na bai daya, kana su sauke nauyin dake wuyansu, na gina al’umma mai makomar bai daya ga dukkanin bil adama. Kaza lika su zamo ginshikin ingiza zaman lafiya, da ci gaban bai daya, da koyi daga wayewar kan juna.
Bugu da kari, Xi Jinping ya jaddada cewa, kasarsa za ta goyi bayan karin kasashen duniya masu saurin ci gaba, da masu tasowa, wajen shiga tafiyar BRICS, da tattaro karfin su, da shiga aikin ingiza gina al’umma mai makomar bai daya ga daukacin bil adama. (Mai fassara: Saminu Alhassan)