Kamfanin rarraba wutar lantarki na Nijeriya ya ce, ma’aikatansa sun gano matsalar da ta haddasa katsewar wutar lantarki a layin Ugwuaji-Apir mai karfin kilo 330 (kV)
A ranar Talata, TCN ta ba da rahoton katsewar wutar lantarki a Arewa-Maso-Gabas, Arewa-maso-Yamma, da kuma wasu sassan Arewa ta Tsakiya, bayan layukan watsa wutar lantarki mai karfin 330kv na Ugwaji-Apir 1 da 2 sun tsayar da bayar da wuta da misalin karfe 4:53 na safe “Sakamakon wata matsala ” .
- Gwamnatin Tarayya Ta Tabbatar Da Shirin Kara Haraji
- Gwamnatin Tarayya Ta Tabbatar Da Shirin Kara Haraji
Katsewar wutar lantarkin ta faru ne a ranar Litinin.
Da yake bayar da karin haske a cikin wata sanarwa a ranar Laraba, babban manajan kamfanin, Ndidi Mbah, ya ce an gano matsalar ne a dajin Igumale na jihar Benue.
Kamfanin ya ce, tawagar masu kula da layukan wuta na TCN ne suka gano matsalar a kan layin da misalin karfe 5 na yammacin Laraba.