Babban Bankin Najeriya (CBN) ya bayyana cewa ba shi da wani shirin dakatar da amfani da tsofaffin takardun Naira.
Wannan sanarwa ta fito ne domin musanta rahotannin da ke cewa tsoffin takardun N200, N500, da N1,000 za su daina zama halastaccen kuɗi nan da 31 ga Disamba, 2024, bayan da Majalisar Wakilai ta buƙaci bankin ya samar da sabbin takardun kuɗin.
- CBN Ya Kaddamar Da Sabbin Ka’idoji Ga Masu Harkar POS
- CBN Ya Sake Nanata Ba Da Kariya Ga Kudaden Ajiya A Bankuna
CBN ya jaddada cewa hukuncin Kotun Koli na Nuwamba 2023, wanda ya bayar da izinin amfani da tsoffin takardun ba tare da lokaci ba, har yanzu yana nan daram. Bankin ya tabbatar wa ‘yan Nijeriya cewa dukkan tsoffi da sabbin nau’ikan takardun Naira za su ci gaba da kasancewa a matsayin halastaccen kuɗi a faɗin ƙasa.
Muƙaddashin Daraktan hulɗa da Jama’a, Hakama Sidi, ya shawarci ‘yan Nijeriya su ci gaba da karɓar dukkan takardun Naira tare da la’akari da amfani da hanyoyin biyan kuɗi na lantarki don rage dogaro da kuɗin hannu.