Jami’an hukumar tsaron Farar Hula ta Nijeriya (NSCDC) sun cafke wani da ake zargi mashahurin dan bindiga, Umar Ibrahim, wanda aka fi sani da Danlami Tela, a Jihar Kano.
Kakakin hukumar, SC Ibrahim Idris Abdullahi, ya bayyana cewa an kama wanda ake zargin mai shekaru 45 a ranar 24 ga Oktoba, 2024, a unguwar Hotoro Yandodo da ke yankin ƙaramar hukumar Nassarawa.
- Gwamnan Kano Ya Taya Kwankwaso Murnar Cika Shekara 68 Da Haihuwa
- Sarki Sanusi II Zai Naɗa Babban Ɗansa A Matsayin Ciroman Kano
Binciken farko ya nuna cewa Ibrahim, wanda ɗan asalin garin Dikke ne a ƙaramar hukumar Funtua ta jihar Katsina, yana da alaƙa da wani babban ɗan bindiga da ke da hannu wajen garkuwa da mutane da aikata ta’addanci a Funtua da kewaye.
Abubuwan da aka samu a hannunsa sun haɗa da waya ta Android, SIM guda uku, da katin cirar kuɗi na bankin Unity.
NSCDC ta Kano, karkashin jagorancin Comdt. Mohammed Lawal Falala, ta mika Ibrahim ga sansanin Sojin saman Nijeriya na Forward Operating Base 215 da ke Funtua domin ci gaba da bincike.
Wannan kuma na cikin matakan hukumar don hana shigowar ‘yan bindiga Kano, bayan kwanan nan ta gudanar da sumame kan maɓoyar miyagun a Katsina, da Kaduna, da kuma Zamfara.
Hukumar ta sake tabbatar da ƙudirinta na tabbatar da doka da oda, inda ta jaddada nasarar kama ‘yan fashi 9 da wasu miyagu 45 a Kano kwanan nan.