Kwanan baya, kwamiti na 3 na babban taron MDD karo na 79, ya kira taron muhawara a hedkwatarsa, inda Amurka, da Austriliya da dai wasu kasashe ‘yan tsiraru suka soki kasar Sin kan batun hakkin Bil Adama ba gaira ba dalili.
Shin ko wane ne yake da ikon bayyana halin da ake ciki game da wannan batu? Ba shakka jama’a ne da kan su. Sinawa da yawansu ya kai biliyan 1.4 sun fita daga kangin talauci, har ma sun samu wadata tare, suna more rayuwarsu, suna zama cikin kwanciyar hankali, wannan shi ne hakikanin ci gaba a fannin kare hakkin Bil Adam.
A wani bangaren na daban, bari mu duba Amurka da Austriliya. Amurka ta dade tana fama da matsalar nuna bambancin launin fata, kana yawan mutanen da suka mutu sakamakon harin bindiga a kasar ya kai kimanin dubu 43 a shekarar 2023 kadai. A sa’i daya kuma, a kalla mutane 1,247 sun mutu a kasar, sakamakon nuna karfin tuwo da ‘yan sanda suke yi. A Austriliya fa? kowa ya san cewa kasar ta samu ci gabanta ne ta hanyar cin zarafin mutane ‘yan asalin wurin da aka kafa kasar.
Wadannan kasashe ba su kula da rayuka, da zaman rayuwar jama’arsu ba, balle na al’ummun sauran kasashe. Yanzu haka, a zirin Gaza, fararen hula fiye da dubu 40 sun mutu, miliyoyin mata da kananan yara na fama da yunwa da rashin muhallin zama. Ba shakka, wannan wuri na matukar bukatar kare hakkin al’ummun sa. Amma, jami’i mai kula da harkokin jin kai a zirin Gaza na kasar Amurka, ya yi ikirarin cewa, gwamnatin Amurka ba za ta daina samarwa Isra’ila makamai ba, duk da cewa matakan da ta dauka a Gaza sun sabawa dokar kasa da kasa.
Marigayi masani Publius Cornelius Tacitus, wanda ya mutu a shekaru 2000 da suka gabata, ya taba bayyana cewa, “An nunawa mutane baraguzan gine-gine sun ce wannan shi ne zaman lafiya”, yanzu wasu kasashen yamma suna kokarin ta da rikici a wasu wurare, inda mutane ke fama da asarar rayuka da dimbin wahalhalu, amma sun mai da kansu masu koyar da mutanen duniya dabarar kare hakkin Bil Adam, gami da shafawa kasar Sin bakin fenti, duk da iyakacin kokarin da kasar ke yi a fannin kare hakkin da ikon jama’arta.
Sai dai wadannan kasashen ba za su iya mai da fari baki ba. Ko da yake sun dade suna kokarin dora laifi kan kasar Sin, kan batun hakkin Bil Adam, amma yawancin kasashe ba su taba yarda da maganarsu ba.
Tabbas, zamani na yin shisshigi cikin harkokin gidan sauran kasashe bisa hujjar kare hakkin Bil Adama ya kai karshensa. (Mai zane da rubutu: MINA)