Majalisar ta yi wata ganawa ta musamman da Hafsoshin Soji da sauran shugabannin hukumomin tsaro na kasar nan, kan lamarin tabarbarewar rashin tsaro da ke ci gaba da yin kamari.
Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Ahmad Lawan, ne ya jagoranci sauran shugabannin kwamitin tsaro na majalisar a zaman ganawar.
- Yajin Aikin ASUU: Kungiyar Dalubai Ta Bukaci A Kori Ministan Ilimi
- Babban Yankin Kasar Sin Ya Dakatar Da Shigar Da Wasu Kayayyaki Daga Taiwan
Shi kuwa Babban Hafsan Hafshoshin Sojin Nijeriya, Janar Lucky Irabor ne, ya jagoranci sufeto ‘yan sanda da na NIA da na DSS da kuma na NSCDC.
Mai bayar da shawara kan tsaron kasar nan Manjo-Janar Babagana Monguno ne, wakilce shi ne a wurin taron saboda ya na kan halartar tsaron majalisar zartaswa ta tarayya.
A jawabinsa kafin zaman, Sanata Lawan ya ce, majalisar ta kira zaman, inda ya sheda wa manyan jami’an tsaron cewa majalisar ta yi iya namijin kokarinta kamar yadda bangaren twamnatin tarayya ya yi wajen amince wa da kudade domin a dakile kalubalen rashin tsaro a kasar.
Ya ce, an kira zaman ne, don a lalubo mafita kan kalubalen rashin tsaro a kasar.
Ya ci gaba da cewa, “Kafin majalisa ta tafi hutu a makon da ya gabata, mun tattauna kan kalubalen rashin tsaro a baya, mun tattauna a zaman majalisar daban-daban kan kalubalen
“Majalisar mai ci yanzu da kuma wacce ta gabata a baya, ta yi iya nata kokarin kan kalubalen.
“Babu wani mulki a kasar, musamman tun daga lokacin Jamhuriya ta hudu da ta fara a 1999 da ya narka kudade kan tsaro kamar yadda gwamnati mai ci a yanzu ta yi.
“Muna fatan daga wannan zaman na yau, lamarin rashin tsaro a kasar zai ragu, na san shugabannin hukumomin na tsaro suna yin iya nasu kokarin amma akwai bukatar a kara jajircewa don a tsawo kan kalubalen.”
A nasa jawabin Janar Irabor ya gode waajalisar kan gayyatar wacce ya danganta a matsayin tattaunawar cikin gida domin a samu fahimtar juna.
A cewarsa, abubuwa da dama sun faru, an yi abubuwa da dama domin a habaka tsaro a kasar nan.