Hukumar da ke kula da ayyukan kafafen watsa labarai (NBC), ta ci tarar gidan talabijin na Trust (Trust TV) Naira miliyan biyar saboda watsa ayyukan ‘yan ta’addan jihar Zamfara.
Hukumar, a wata takarda mai dauke da sa hannun darakta-janar dinta Balarabe Shehu Illela, ta ce ta ci tarar Trust TV ne saboda ta watsa rahoto na musamman da ya saba ka’idojin hukumar.
- 2023: PDP Ta Bukaci A Hana Gwamnan Gombe Da Mataimakinsa Takara Kan Zargin Gabatar Da Takardun Bogi
- 2023: Fintiri Ya Zabi Mace A Matsayin Abokiyar Takararsa
Sai dai kamfanin Media Trsut ya ce a “Yayin da muke ci gaba da nazari kan matakin hukumar da kuma duba zabukan da muke da su, muna sanar da cewa a matsayinmu na gidan talbijin, mun yi amannar cewa muna aiki ne domin al’umma ta hanyar karin haske kan batun garkuwa da mutane mai sarkakiya da kuma yadda yake shafar miliyoyin jama’ar kasarmu.”
Sanarwar ta kara da cewa rahoton ya bi salsalar zaman dar-dar a tsakanin al’umma da kuma abubuwan da suka sanya rikicin da ya sa wasu ke daukar makamai da ke jefa mutane cikin mawuyacin hali.
Rahoton ya fito da matsalolin rashin adalci da kabilanci da rashin iya gudanar da mulki wadanda su ne ke haddasa irin wannan rikici.
Hakazalika ya bayar da shawara kan yadda za a magance matsalolin ta hanyar tattaunawa da masana da masu ruwa da tsaki, ciki har da Ministan Yada Labarai, Alhaji Lai Mohammed, da Sanata Saidu Mohammed Dansadau, da Farfesa Abubakar Saddique na Jami’ar Ahmadu Bello, da sauransu.
A makon da ya gabata ne gwamnatin tarayya ta yi Allah wadai da matakin da BBC da kuma Trust TV suka dauka na watsa rahoton na musamman kan ayyukan ‘yan bindiga.