Rahotanni sun bayyana cewa wasu shugabannin siyasa a yankin arewa sun shiga rudani wajen lalubo dan takarar da za su mara wa baya a zaben shugaban kasa mai zuwa, domin kalubalantar Shugaban kasa Bola Tinubu.
An bayyana cewa wasu daga cikin shugabannin arewa ba su gamsu da halin da al’ummar kasar ke ciki ba, wanda a tunaninsu lamarin ya fi tasiri a yankin arewa. Rahotanni sun nuna cewa shugabannin siyasan a arewa sun ce gwamnatin Shugaba Tinubu ta yi watsi da su, duk da goyon bayan da suka bayar a zaben da ya gabata, suna masu ikirarin cewa arewa ba ta ci gajiyar abin da ake tsammani ba.
- Ba Zan Goyi Bayan Ƙudirin Ƙarin Haraji Ga Talakawa Ba – Sanata Ndume
- EU Za Ta Janyowa Kan Ta Lahani Sakamakon Kakaba Karin Haraji Kan Motoci Masu Aiki Da Lantarki Kirar Sin
Duk da cewa zaben 2027 ya rage saura ‘yan shekaru kadan, amma an bayyana cewa dattawan arewa na kara zage dantse wajen lalubo zaratan ‘yan takara masu nagarta don kalubalantar shugabanni masu ci a yanzu. Wasu fitattun ‘yan siyasa a yankin arewa maso yamma sun yi taro wajen tattaunawa kan dan takarar da zai iya doke Shugaba Tinubu a zaben 2027.
Haka kuma wasu masu taimaka wa gwamnonin arewa sun tabbatar da wannan tattaunawa, inda suka yi nuni da cewa, zaben 2027 ne ke gaban manyan ’yan siyasar arewa da suka hada da shugabanninsu. Rahotanni sun bayyana cewa wadannan ‘yan siyasan na auna hadarin da ke tattare da adawa da Shugaba Tinubu bayan ya samu nasara a zaben 2023.
Wani kalubalen da ke gaban shugabannin arewa shi ne, zaben dan takarar da zai samu karbuwa sosai a arewa tare da yin la’akari da dabarun adawa, kamar jaddada tsarin shiyya-shiyya da muradun Kudu.
“Su shugabannin arewa sun yi imanin cewa hanya mafi dacewa ita ce a goyi bayan fitaccen dan siyasar kudu,” in ji wata majiya, “amma duk da haka sun damu wajen lalubo wani daga kudu da zai dace da Shugaba Tinubu a matsayinsa da kuma karfin kudi.”
Duk da cewa ba a yanke hukunci a hukumance ba, majiyoyi sun ce an fara fitar da jerin sunayen ‘yan takara da kuma mataimakansu
“Watakila za a zabi wani sahihanci dan siyasa daga yankin arewa maso yamma a matsayin abokin takara,” in ji wata majiya mai tushe, inda ta bayyana cewa Dakta Rabi’u Musa Kwankwaso, tsohon gwamnan Jihar Kano, da Alhaji Aminu Tambuwal suna cikin sunayen da aka zayyana.
“A halin yanzu, ‘yan siyasar arewa na ci gaba da neman wanda zai iya tsayawa takara a 2027. Duk da haka, zai yi wuya su sake mara wa wannan gwamnati baya,” in ji majiyar, lamarin da ke nuni da cewa har yanzu siyasar arewa ta yi nisa.
Bugu da kari kan nuna damuwa da yadda wannan gwamnati ke kara samun rashin inganci, rahotanni sun nuna cewa shugabannin arewa sun yi taka-tsan-tsan game da koma bayan da ‘yan mazabarsu za su iya fuskanta idan suka ci gaba da mara wa Shugaba Tinubu baya a 2027.
Kasancewar rashin aikin yi da hauhawar farashin kayayyaki da rashin tsaro da ke addabar al’ummar arewa, shugabannin na fargabar cewa amincewa da shugabancin da ba a canza ba zai iya raba kan matasa.