A wannan lokaci da duniya ke fuskantar yanayi na saurin fadadar ci gaban fannonin kimiyya da fasaha, da takara mai tsanani tsakanin sassa daban daban, ko shakka babu kasar Sin ta ciri tuta, wajen zama ginshiki mai karfi a bangaren cin gajiyar fannonin kimiyya da fasaha daban daban, wanda a ganin masharhanta da dama, hakan ya samar da dama ga daukacin duniya na cin gajiya tare.
To sai dai kuma, a hannu guda matakin Amurka na baya bayan nan, na hana Amurkawa zuba jari a wasu sassan kimiyya da fasaha na kasar Sin, ya haifar da tarnaki ga cin gajiya tare tsakanin kasashen biyu, kana hakan ya nuna rashin fahimtar Amurka game da ainihin halin da duniya ke ciki ta wannan fanni.
- An Yanke Wa Mai Haƙar Ma’adanai Hukuncin Shekara 1 Saboda Satar Waya
- Gwamna Sani Ya Amince Da ₦72,000 Mafi Ƙarancin Albashi Ga Ma’aikatan Jihar Kaduna
Sanin kowa ne cewa, Sin ta riga ta cimma wani mataki mai nisa na ci gaban kimiyya da fasaha, wadanda ake iya gani a zahiri idan an bibiyi mujallun yada ilimi, da makaloli, da sakamakon ayyukan bincike daban daban. Hakan ne ma ya sa hukumar lura da kare ikon mullakar fasaha ta kasa da kasa ko WIPO, ta ce Sin din ce kan gaba a duniya wajen yawan masu gabatar da bukatun rajistar mallakar fasaha. Alal misali, a shekarar 2019, Sin ta tsallake Amurka wajen zama kasa ta daya a duniya, da alummar ta suka gabatar da mafi yawan irin wadannan bukatu na rajista.
Don haka matakin Amurka na kakaba takunkumin zuba jari a kasar Sin, a fannonin samar da sassan hada latironi ko semiconductors, da fannin kirkirarriyar basira ko AI, da fasahar manyan lissafi da na’urori masu kwakwalwa ko quantum technology, zai illata ita kanta Amurkan.
Don haka a gani na, maimakon Amurka ta dauki irin wadannan matakai na “A fasa kowa ya rasa”, ko fito na fito, kamata ya yi ta rungumi dukkanin wasu hanyoyi na raya hadin gwiwa, ta yi tarayya da Sin a matsayin abokiyar gudanarwa, da cin gajiyar sakamakon da Sin ke samu a fannin raya ilimin kimiyya da fasaha.
Sassan biyu suna iya cimma hakan ne kawai, idan sun rungumi juna, sun yi aiki tare a fannonin bincike, musayar fasaha, da raba kwarewa, musamman a bangarorin nazarin sauyin yanayi, kiwon lafiya, da sauran bukatun bil adama na bai daya.