Gwamnatin Tarayya ta ƙaddamar da nau’in kajin gida guda biyu da kuma nau’in (iri) amfanin gona 14 domin bunƙasa aikin gona da inganta abinci a Nijeriya.
An bayyana wannan cigaba a yayin taron kwamitin kasa na 34 na ba da sunaye, da rajista, da ƙaddamar da nau’in amfanin gona, da dabbobi da kuma kifi.
- Cututtukan Da Suka Fi Addabar Kajin Gidan Gona Lokacin Damina
- Gidauniya Da Gwamnatin Zamfara Sun Tallafa Wa Mata 200 Da Kajin Kiwo
Shugaban kwamitin, Farfesa Soji Olufajo, ya sanar da samar da sabbin nau’i kan bisa ga shawarwarin kwamitin da ke ƙunshe da masana, da ‘yan bincike, da masu kula da ilimin jinsin dabbobi da tsirrai.
Sabbin Kajin gida, da Noiler da Cobb 500, tare da nau’in iri masu yawan samar da kayan amfanin gona kamar alkama, da sha’ir, da masara, a rogo, da shinkafa, da conchorus, sun zo domin ƙara yawan amfanin gona da fa’idar abinci.
Darakta janar na cibiyar samar da albarkatun Jinsunan halittu da fasahar kwayoyin halitta (NACGRAB), Dakta Anthony Okere, ya yi kira ga manoma da su rungumi wannan cigaba domin bunƙasa yawan amfanin gona da tabbatar da wadatar abinci.
Wannan matakin zai buɗe hanya ga masu kiwon kaji da masu bincike su amfana da sabbin nau’in dabbobi da amfanin gona.