Hanyoyin Nijeriya sun zama hanyoyi masu ban tsoro masu cinye rayukan jama’a. Daga cikinsu akwai na kwana kwanan nan, hatsarin da a ka yi a Kaduna inda mutum arba’in suka rasu a kan hanyar su ta zuwa wurin bilin maulidi.
Motar da suke ciki ne ta yi taho mu gamu da wata tankar mai a hanyar Saminaka kta kramar hukumar Lere, a Jihar Kaduna.
- EFCC Za Ta Binciki Yadda Kudaden Kananan Hukumomi Ke Sulalewa
- Shugabannin Sin Da UAE Sun Taya Juna Murnar Cika Shekaru 40 Da Kafuwar Huldar Diflomasiyya Tsakaninsu
Kwanaki kadan kafin wannan, wani mummunan hatsarin ya afku a Jihar Neja inda ya yi sanadiyyar rasuwar mutum arba’in da takwas bayan wata takar mai ta hade da tifa wanda ya yi sanadiyyar mummunar fashewa.
Wata daya kafin wannan nan, an samu hatsari kashi daban-daban a Jihar Oyo da Ogun inda mutum talatin da bakwai da ashirin da biyar suja rasu a rana guda a babban hanyar Ibadan zuwa Legas.
Wannan ba kawai kididdiga ba ne, wannan yana nuna da yadda mutane ke rasa rayukansu ta hanyar da za a iya kiyayewa.
Duk da yadda yawan adadin mutanen da suke rasuwa ta hanyar hatsari ya ragu a shekara 2023, da kimanin mutum 5,081 idan a ka kwatanta da mutum 6,456 da suka rasu a shekarar 2022, kamar yadda hukumar kula da hanyoyi a Nijeriya ta bayyana.
Nijeriya tana cikin kasashe masu yawan mutuwa a kan tituna a duk duniya da kaso 33.7 a cikin mutum 100,000 wanda ya wuce yadda ya kamata wato kaso 17.4.
Mu dawo dashi daidai, kason da ya kamata ya tsaya a duniya shi ne, 17.4 duk mutum 100,00. Inda kasar Zimbabwe take kan gaba da kimanin mutuwa 74.5 duk mutum 100,000.
Dililan da suke janyo wannan mace-macen a kan hanyoyi sannannu ne kuma kididdigaggu. Gudun wuce iya kima ka yana kan gaba inda direbobi suke wuce iyakan da aka sanya domin samun riba mai yawa musamman a motocin haya.
Tukin ganganci, gajiya, da kuma oba lod a motoci da kuma tuki cikin dare ne suke kara girmama hatsarin.
A ‘yan shekarun nan, yawan anfani da wayar hannu a lokacin tuki ya kara munana lamarin. Inda direbobin da hankalinsu ya dauke suke jawo hatsari. Ko ta hanyar daukar waya, tura sakonni, ko kuma duba shafukan sada zumunta, wadannan abubuwan da ke dauke hankali sun nuna suna da hatsari sosai.
Lalacewar hanyoyin Nijeriya kuma yana kara hauhwar matsalar. Manyan tituna sun lalace da ramuka, kuma ba tare da alamun hanya masu kyau ba inda hatta direbobi masu kiyayewa ke iya fadawa cikin hatsari.
Duk da ana yawan zargin direbobi masu zaman kansu, lalacewa da kuma rashin gyara da kuma kawo karshen lalatattun hanyoyi na cikin abubuwa masu tada hankali.
Abun takaicin shi ne masu kula da dokokin hanya sun mayar da hankalinsu wajen kananan abubuwan da basu da muhimmanci kamar takardun mota, inda suka maida shi hanyar samun kudi maimakon wajen kare rayukan mutane.
Tsaffin hanyoyin magance hadurran da muke amfani dasu sun gaza. A wasu kasashen duniya kimiyya ya taka rawar gani wajen magance mace mace a hanyoyi ta hanyar anfani da kamarorin duba gudu da kuma na’urorin agajin gaggawa. A Nijeriya, wadannan ci gaba sun karanta, hakan yake barin hanyoyin a lalace fiye da yadda ya kamata su zama.
Ilimin direbobi shi ma babban abin lura ne. Hanyar samun lasisi a Nijeriya cike yake da cin hanci, hakan yake barin direbobin da basu cacanta ba suna samun lasisi ba tare da horon da ya dace ba. Ya kamata a sauya tsarin samun lasisin, a kuma maida hankali wajen ilmantarwa, gwaji da kuma horar da direbobin.
Mace-macen rayuka a kan hanyoyi na tada hankali. Hatsari a hanyoyi ya zama hanya na biyu da yake kawo mace mace wanda ya wuce ayyukan Boko Haram da ‘yan ta’adda. Duk da an maida hankali wajen. wadancan kalubalen, mace-macen da a ke samu a hanyoyi shi ma yana da tayar da hankali.
Hatsarruka na da tasiri a fannin tattalin arziki. Asibitoci, sun riga sun cika kuma babu isasshen kayan aiki ga majinyantan hatsarruka a kwance. Iyalai na fuskantar barazana ta hanyar rasa jigogin iyalin, kasuwanci na samun tsaiko wajen samun kayayyaki da kuma tafiyar ma’aikata.
Wadannan su ne hanyoyin da ta kamata gwamnati ta dauka, na farko, zuba jari da kuma manyan ayyuka a hanyoyi. Manyan hanyoyi na bukatar gyara a kai a kai, dole a gyara ramuka, a samar da wuta, da kuma alamun nuni a hanyoyi. Wadannan ci gaban za su iya samar da gagarumin sauyi wajen kare afkuwar hadurra.
Kimiyya da fasaha na taka rawar gani wajen kiyaye hadurra. A samar da kamarori, musamman a wajen da suke da hadari, wannan zai rage guje guje da kuma tukin ganganci. A kuma samar da wajen samar da agajin gaggawa a kusa da manyan hanyoyi su zama a shirye wajen kawo dauki idan an samu hadurra.
Tsaurara dokin tuki a hanyoyi shima wani babban hanya ce. Hukumar Kare Hadurra da sauran masu sa ido dole a samar masu da kayan aiki kuma a sa masu ido domin tabbatar da suna aiki yadda ya kamata. Wannan ya hada da kama masu gudun ganganci, masu shaye shaye yayin tuki, da kuma masu yin wasu abubuwa yayin da suke tukin. A samar da tara ga duk wanda ya karya dokokin ya zama mai tsanani saboda ta zama izinina ga saura. Sannan kuma a dauki mummunan mataki a kan masu nanata laifi.
Ilimin direbobi na da matukar muhimmanci, wannan hanyar samun lasisin dole a canza shi da tsari mai kyau wanda kuma za a tabbatar da bin doka a ciki. Ya zama direbobi na fuskantar tantancewa, da kuma horo wa da zai sanya masu al’adun tuki a tattare dasu. A kuma tsananta wayar da kan jama’a masu anfani da hanyoyi a kan hadurra da kuma yadda ganganci ke jawo hatsari.