Hukumar kula da kwallon kafa ta nahiyar Afrika CAF ta sanar da cewa za a gabatar da bikin kyautar gwarazan dan wasan Afrika ta shekara ta 2024 a birnin yawon bude ido na Marrakesh da ke kasar Moroko.
Kuma an tsara za a gudanar da kyautar ne a ranar 16 ga watan Disambar 2024 a cikin wani sako da ta wallafa a shafinta na D, CAF ta sanar da cewa lokaci ya sake zagayowa domin gudanar da wannan bikin na shekara-shekara.
- EFCC Za Ta Binciki Yadda Kudaden Kananan Hukumomi Ke Sulalewa
- MDD Za Ta Yi Duk Mai Yiwuwa Wajen Taimaka Wa Nijeriya Kawo Karshen Talauci
Wannan ne karo na biyu a jere da ake gudanar da bikin a birnin na Marrakesh, karo na uku kuma da ake yi a kasar Moroko sannan CAF ta ce za ta tabbatar da lokacin da za a fara kyautar ta 2024 da zarar lokaci ya yi.
Wanda ke rike da kambun kyautar ta bangaren maza shi ne dan wasan Najeriya na gaba, Bictor Osimhen sai a bangaren mata kuwa takwararsa da Najariya Asisat Oshoala ce ke rike da kyautar ta shekara ta 2023.
Kyautar tana mayar da hankali ne kan kokarin da ‘yan wasa ke yi a kasarsu da kuma kungiyoyin da suke bugawa kwallo, domin bayar da wannan kyauta mai daraja ta gwarazan Afrika bangaren maza da mata ta shekara.
Dabi Alonso Zai Maye Gurbin Ancelotti A Real Madrid
Wasu rahotanni daga kasar Spaniya sun bayyana cewa tuni shugaban gudanar da kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid Florentino Perez ya yi umarnin fara shirye-shiryen tarbar mai koyarwa Dabi Alonso a kakar wasa mai zuwa.
Bayanai sun ce Perez a fusace ya ke da yadda Ancelotti ke tafiyar da kungiyar a yanzu haka, duk da zuwan zakakuran dan wasa irinsu Kylian Mbappe na Faransa, wanda ya koma kungiyar daga PSG a farkon wannan kakar.
A cewar rahotannin, hatta ranar Asabar din da ta gabata ya yin wasan hamayya na El Classico anga fushi karara a fuskar Perez bayan ruwan kwallayen da tawagar ta Ancelotti ta sha a hannun babbar abokiyar hamayyarta, Barcelona.
Bayan rawar da Ancelotti ya taka a kakar da ta gabata ne, Perez ya amince da tsawaita kwantiraginsa zuwa shekara ta 2026 sai dai shugaban a yanzu ya fara saka shakku ganin koma bayan da kungiyar ke gani watakila ko saboda yawan shekarun kociyan dan asalin kasar Italiya wanda ya lashe kofin zakarun Turai har guda 3 ga kungiyar.
Baya ga batutuwa masu alaka da raguwar karsashin Real Madrid, Carlo Ancelotti na rikici da mahukuntan kungiyar kan batutuwa da dama ciki har da sabunta kwantiragin Mendy da kungiyar bata so ba amma Ancelotti ya kafe, sai kuma alkawuran kocin game da makomar Arda Guler dan Turkiya, dan wasan da baya samun dama karkashin manajan.
A bangaren mai koyarwa Alonso, duk da cewa tsirarun masu koyarwa ne ka iya cewa a’a ga Real Madrid amma ana ganin abu ne mai wuya kungiyar ta iya shawo kan sa cikin sauki lura da cewa a watan Yunin da ya gabata ne ya sabunta kwantiraginsa kuma kungiyoyi da dama sun nemi aiki da shi amma ya juya musu baya.