ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Monday, December 22, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Ɗaliban Cyprus: Zamfara Ta Samar Wa Ɗalibanta ‘Yanci Da Ke Karatu A Gida Da Ƙetare

by Leadership Hausa and Sulaiman
1 year ago
Cyprus

A ranar 29 ga watan Mayun 2023 Gwamna Dauda Lawal ya karɓi jagoranci a hannun gwamnatin da ta kasa biyan kuɗaɗen jarabawar ɗalibai har na shekaru uku, wanda hakan ya kange ɗaliban jihar Zamfara daga ɗaukar jarabawar WASSCE da na NECO.

 

Matsalolin Rashin biyan kuɗaɗen karatu na makarantu daban-daban na ɗaliban jihar Zamfara da ke karatu a Cyprus da India, suna daga cikin ɗimbin matsalolin da wannan gwamnati ta gada daga gwamnatin da ta gabata.

ADVERTISEMENT
  • An Zargi ‘Yar Siyasa Da Yunkurin Kashe Shugaban Kasar Malawi
  • Trump Da Magoya Bayansa Sun Yi Amfani Da Kalaman Batanci

Game da ɗaliban da ke karatu India da Sudan, gwamnatin jihar Zamfara ta shirya da jami’o’in. Zamfarawan da ke kataru a Indiya har sun kammala karatun su, yanzu haka ma suna shirye-shiryen dawowa gida.

 

LABARAI MASU NASABA

An Sako Ragowar Ɗalibai Da Malamai Da Aka Sace A Makarantar Katolika Ta Neja

Akpabio, Ganduje, Ogundoyin Sun Halarci Naɗa Seyi Tinubu Sarauta

Sakamakon yaƙin da ake yi a Sudan, yanzu haka an samu nasarar kwaso ɗaliban Zamfara 66. Amma kuma 14 daga cikinsu, masu karatun Nas-nas, ba su samu samar ɗaukar jarabawar ƙarshe ba. Gwamnatin jihar Zamfara, tare da haɗin gwiwa da Jami’ar Sudan, ta shirya wa ɗaliban 14 jarabawa a wata cibiyar da ba ta Jami’ar ba a nan Nijeriya. Gwamnatinmu ta ɗauki nauyin kuɗin jirgi, wurin kwana da abinci na Malamai uku daga Sudan da suka gudanar da jarabawar ɗaliban 14. Dukkan ɗaliban 14 sun zana jarabawarsu ta ƙarshe, sauran ɗaliban 52 kuma gwamnati ta ɗauki nauyin su a wasu Jami’o’i a Nijeriya.

 

Mun kafa tarihi ta hanyar warware irin waɗannan matsalolin da ɗaliban Zamfara suka fuskanta a Indiya da Sudan ta hanyar shiga tsakanin na gwamnatin jiha. Tambayar ita ce: Me ya sa Jami’ar Ƙasa da Ƙasa ta Cyprus ta bambanta?

 

Duk da ɗimbim matsalolin da aka samu a lokacin da aka tura ɗalibai zuwa Cyprus da wasu ƙasashe, gwamnatin jihar na bin dukkanin hanyoyin da suka dace don magance matsalar, amma mahukuntan makarantar na daƙile yunƙurin.

 

A ranar 12 ga Nuwamba, 2023, gwamnatin jihar ta biya jami’ar Naira Miliyan 84.7. Bayan kwana biyu, a ranar 14 ga Nuwamba, 2023, an sake tura Naira Miliyan 30.9 zuwa makarantar.

 

Jami’ar ƙasa da ƙasa ta Cyprus ta ci gaba da yin watsi da buƙatar gwamnatin jihar na aikewa da tawaga domin tattauna batutuwan da suka shafi ɗaliban mu da ake ba su tallafin karatu. Don haka sai da gwamnatin jihar ta tuntubi ofishin jakadancin Nijeriya da ke Turkiyya domin neman taimako.

 

A watan Mayun 2024, bayan gagarumin matsin lamba daga Ofishin Jakadancin Nijeriya na Ƙasashen Waje a Turkiyya, hukumomin makarantar sun sanar da gwamnatin jihar cewa, a shirye suke su karɓi tawaga a jami’ar da ke Cyprus, dangane da miƙa kuɗaɗe don nuna cewa da gaske ta ke. Sakamakon haka, a ranar 4 ga Yuni, 2024, gwamnatin jihar ta aika da Naira miliyan 100 kamar yadda jami’ar ta buƙata.

 

Dangane da haka ne Gwamna Dauda Lawal ya kafa wata tawaga mai mutane uku domin tafiya Jami’ar Cyprus. Tawagar ta haɗa da Mallam Wadatau Madawaki, Kwamishinan Ilimi, Kimiya da Fasaha; Bello Mohammed Auta, Kwamishinan Kuɗi; da Barau Muazu, Mai Bai Wa Gwamna Shawara na Musamman Kan Harkokin Kuɗi da Tattalin Arziki.

 

Tawagar ta na da alhakin tabbatar da haƙiƙanin adadin kuɗaɗen da jihar Zamfara ke bin jami’ar dangane da ɗalibai 93 da aka tura tallafin karatu tun daga shekarar 2019; a tantance dukkan ɗaliban jihar Zamfara da ke jami’ar da kansu don sanin haƙiƙanin adadinsu; don tabbatar da irin kwasa-kwasan da ɗalibai ke ɗauka, don tabbatar da shekarar kammala karatun kowane ɗalibi.

 

Sauran ayyukan sun haɗa da ganowa da tantance yanayin da ake gudanar da karatun, halin da gidajen kwanan ɗaliban suke, ciyarwa da sauran abubuwan da suka danganci ilmantarwa da samar da ababen more rayuwa, da samar da yarjejeniyar fahimtar juna don daidaita al’amura.

 

Kafin barin Nijeriya, tawagar ta tuntubi ofishin jakadancin Nijeriya da ke ƙasar Turkiyya, wanda hakan ya sa wasu jami’an ofishin guda biyu suka shiga tawagar zuwa ƙasar Cyprus a ranar 14 ga Agusta, 2024, domin kammala ayyuka da aka lissafa a sama. A ranar 15 ga watan Agusta, sun gana da ɗaliban da kuma Hukumar Gudanarwar Jami’ar, inda suka warware matsalar

 

Ganawar farko da hukumar ta yi da Farfesa Majid, tawagar ta buƙaci a aiwatar da duk wata yarjejeniyar fahimtar juna tsakanin Jami’ar Cyprus da Gwamnatin Jihar Zamfara, wanda ya haɗa da; jimillar bashin da ake bin kowane ɗalibi daga farko har zuwa yau, wanda ƙunshi adadin kuɗin da ake bi a kowane zangon karatu, kuɗaɗen da aka fara biyan da raguwar kuɗaɗen; jimlar karatun ɗalibai a kowane zangon karatu tare da ranar kammala karatun ɗaliban da suka biya kuɗin da kansu don guje wa tsayawar zangon karatu, adadin da aka biya wa kowane ɗalibi da jimillar duka kuɗaɗen.

 

A ganawar da ta yi da shugaban jami’ar Farfesa Habil Nadiri, tawagar ta gabatar da batutuwa da dama da ɗaliban jami’ar ke fuskanta, waɗanda suka haɗa da rashin rijistar ɗalibai domin ba su damar halartar laccoci da kuma samun kayayyakin makaranta don gudanar da karatunsu yadda ya dace; korar ɗaliban gaba ɗaya (sai dai mata goma) waɗanda ke maneji a ɗakin kwanan ɗalibai maza na makarantar; hana dukkan ɗalibai (ciki har da mata goma) abinci daga wurin cin abincin makarantar tun ranar da aka kore su daga ɗakin kwanan ɗalibai.

 

Sauran batutuwan da aka gabatar wa mahukuntan makarantar sun haɗa da sanya wa ɗaliban jihar Zamfara laƙabi da “a ƙarƙashin dokar korar ɗaliban,” wanda aka koka da shi a matsayin hukunci mai tsauri tun da ba su yi wani laifi ga jami’a ko ƙasa ba, da kuma korar ɗaya daga cikin ɗaliban ba tare da sanar da gwamnatin jihar Zamfara ko ofishin jakadancin Njjeriya da ke Ankara ba. Mun kuma yi tir da wannan matakin da aka aiwatar ba gaira ba dalili.

 

Tawagar Zamfara ta bankaɗo rashin daidaito a jami’ar Cyprus. Ofishin babban sakataren ya bai wa gwamnati Yuro 947,544.71 a matsayin jimillar kuɗaɗen da jami’ar ke bin Jihar Zamfara.

 

Ofishin babban mai ba da shawara ga kwamitin amintattu kuma shugaban Sashen Habaka Al’amuran Ƙasa da Ƙasa ya ba da jimillar basussukan da ake bin jihar ke bi kamar Yuro 650,730.24.

 

Ofishin Harkokin Ƙasa da Ƙasa ya tabbatar da cewa ofishin Babban Sakatare bai sabunta tsarinsa ba tare da biyan kuɗi da yawa. Mun yi nazari kan jimillar adadin da ofishin kula da harkokin ƙasa da ƙasa ya bayar kuma mun gano wasu matsaloli da dama da ya kamata a gyara, wanda hakan ya ƙara rage yawan basussuka.

 

Tun bayan dawowar tawagar, gwamnatin jihar Zamfara ta daɗe tana jiran saƙo daga jami’ar Cyprus dangane da adadin kuɗaɗen da ake buƙata domin kawo ƙarshen wannan ka-ce-na-ce.

 

Ofishin Jakadancin Nijeriya a Ankara ya yi aiki tuƙuru don ƙarfafa Ofishin Jakadancin Cyprus don matsa wa Jami’ar Cyprus don samun takardun hukuma. Muna fatan wannan shiga tsakani na diflomasiyya zai taimaka wajen tilasta wa jami’ar yin abin da ya dace ba tare da wata matsala ba.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

An Sako Ragowar Ɗalibai Da Malamai Da Aka Sace A Makarantar Katolika Ta Neja
Manyan Labarai

An Sako Ragowar Ɗalibai Da Malamai Da Aka Sace A Makarantar Katolika Ta Neja

December 21, 2025
Akpabio, Ganduje, Ogundoyin Sun Halarci Naɗa Seyi Tinubu Sarauta
Manyan Labarai

Akpabio, Ganduje, Ogundoyin Sun Halarci Naɗa Seyi Tinubu Sarauta

December 21, 2025
Tashar Teku Ta Ciniki Mai ‘Yanci Ta Hainan Ta Bude Sabon Babin Hadin Gwiwar Sin Da Kasashen Afirka
Ra'ayi Riga

Tashar Teku Ta Ciniki Mai ‘Yanci Ta Hainan Ta Bude Sabon Babin Hadin Gwiwar Sin Da Kasashen Afirka

December 21, 2025
Next Post
Daga Hagu zuwa Dama 1. Aliyu Rabe Aliyu NTA, Nijeriya 2. Abdullaye Koulibaley: Shugaban Hukumar Radio da Telebijin Na Jamhuriyar Nijar 3. Guimbe Kochi Ragiou; Magatakardan Gwamnan Birnin Niamey 4. Hajiya Mariam Lawali Sarki Azbin; Shugabar Kungiyar Yan'jarida Na Afrika masu amfani da Harshen Hausa 5. Mamman Idi Liman 6. Barau Tandja

An Ƙaddamar Da Cibiyar Ƴan Jarida Ta Afrika Masu Amfani Da Harshen Hausa A Nijar

LABARAI MASU NASABA

An Sako Ragowar Ɗalibai Da Malamai Da Aka Sace A Makarantar Katolika Ta Neja

An Sako Ragowar Ɗalibai Da Malamai Da Aka Sace A Makarantar Katolika Ta Neja

December 21, 2025
Raphinha Da Yamal Sun Ci Ƙwallaye Yayin Da Barcelona Ta Doke Villarreal

Raphinha Da Yamal Sun Ci Ƙwallaye Yayin Da Barcelona Ta Doke Villarreal

December 21, 2025
Davido Zai Raƙashe A Bikin Buɗe Gasar AFCON 2025 A Morocco

Davido Zai Raƙashe A Bikin Buɗe Gasar AFCON 2025 A Morocco

December 21, 2025
Yankin Rijiyoyin Mai Na Teku Mafi Girma Na Kasar Sin Ya Ba Da Rahoton Yawan Mai Da Iskar Gas Da Ya Fitar A Shekara

Yankin Rijiyoyin Mai Na Teku Mafi Girma Na Kasar Sin Ya Ba Da Rahoton Yawan Mai Da Iskar Gas Da Ya Fitar A Shekara

December 21, 2025
An Bukaci Bunkasa Fannin Kiwo A Hadin Gwiwar Sin Da Afirka

An Bukaci Bunkasa Fannin Kiwo A Hadin Gwiwar Sin Da Afirka

December 21, 2025
Akpabio, Ganduje, Ogundoyin Sun Halarci Naɗa Seyi Tinubu Sarauta

Akpabio, Ganduje, Ogundoyin Sun Halarci Naɗa Seyi Tinubu Sarauta

December 21, 2025
Tashar Teku Ta Ciniki Mai ‘Yanci Ta Hainan Ta Bude Sabon Babin Hadin Gwiwar Sin Da Kasashen Afirka

Tashar Teku Ta Ciniki Mai ‘Yanci Ta Hainan Ta Bude Sabon Babin Hadin Gwiwar Sin Da Kasashen Afirka

December 21, 2025
Tinubu

Dambarwar Naɗa Muƙamai Da Soke Su A Gwamnatin Tinubu

December 21, 2025
Zaben Fidda Gwani A APC: Sanatocin Jigawa Sun Rasa Tikitin Komawa Majalisa

APC Za Ta Gudanar Da Babban Taronta Na Kasa A Watan Maris

December 21, 2025
Mun Shirya Tsaf Domin Lashe Gasar AFCON Ta Bana – Bassey

Mun Shirya Tsaf Domin Lashe Gasar AFCON Ta Bana – Bassey

December 21, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.